Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Magana kan Nau'in Cutar Ebola da Ya Bulla a Najeriya
- Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta bayyana kwarin gwiwarta kan cewa Najeriya na da karfin shawo kan bullar cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo
- Kakakin shugaban UN, Stéphane Dujarric, ya yaba da matakan gaggawa da hukumomin lafiya na Najeriya suka ɗauka
- Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce majiyyaciyar na karɓar magani a wurin killace masu cutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta bayyana kwarin gwiwarta kan ikon Najeriya na shawo kan bullar cutar Ebola da aka tabbatar kwanan nan.
Majalisar ta kuma yi alƙawarin ba da goyon baya da duk gudummuwar da Najeriya ke bukata domin hana yaɗuwar cutar mai haɗari.

Source: Getty Images
Vanguard ta rahoto cewa kakakin shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, Stéphane Dujarric, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a New York.

Kara karanta wannan
"Ba zai yiwu mu koma baya ba," Gwamna ya yi fatali da yunkurin dawo da tallafin Fetur
UN ta nuna damuwa kan bullar Ebola
Dujarric ya ce majalisar na cikin damuwa game da gano cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo a Najeriya, wadda ta zama ƙasa ta biyar da ta tabbatar da samun bullar cutar a wannan karon.
Sai dai ya bayyana kwarin gwiwarsa kan hukumomin lafiya na Najeriya, inda ya yaba da matakan gaggawa da suka ɗauka da kuma ƙoƙarin gano mutanen da suka yi hulɗa da majiyyaciyar bayan tabbatar da cutar.
“Muna da cikakken kwarin gwiwa kan iyawa da ƙwarewar hukumomin lafiya na gwamnatin Najeriya wajen shawo kan wannan mutum guda da ya kamu da cutar,” in ji shi.
Kakakin ya amince cewa bullar cutar a wata sabuwar ƙasa ta ƙara tayar da hankula kan yiwuwar yaɗuwarta zuwa wasu ƙasashe da ba su kamu ba a baya.
Sai dai ya lura cewa hukumomin Najeriya sun riga sun fara gano mutanen da suka yi hulɗa da majiyyaciyar tare da ɗaukar matakan sanya ido a kansu domin gano yiwuwar kamuwarsu.
UN ta buƙaci haɗin gwiwar ƙasashe
Da aka tambaye shi ko Majalisar Ɗinkin Duniya na fargabar cewa cutar za ta iya yaɗuwa zuwa ƙarin ƙasashe ko kuma ta ci gaba har zuwa wata shekara, Dujarric ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar ƙasashen duniya.
Ya buƙaci ƙasashe su bi ƙa’idojin lafiya na ƙasa da ƙasa tare da yin aiki kafada da kafada da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) domin shawo kan ɓarkewar cutar.
“Yana da muhimmanci ƙasashe su yi aiki tare, su bi ƙa’idojin lafiya na ƙasa da ƙasa, sannan su yi aiki tare da WHO,” in ji shi.

Source: Twitter
Kakakin ya jaddada cewa an kafa WHO ne domin taimaka wa ƙasashe wajen tunkarar irin waɗannan matsalolin gaggawa da suka shafi lafiyar jama’a a duniya.
“Dalilin kafa WHO ke nan, domin taimakawa wajen magance irin waɗannan matsaloli, kuma na san suna mai da hankali sosai kan lamarin,” in ji shi.
Da aka tambaye shi game da tallafin da ake bai wa Najeriya, Dujarric ya sake tabbatar da cewa Majalisar Ɗinkin Duniya a shirye take ta taimaka wa gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan
An gano jirgin da ya ɗauko mai ɗauke da cutar Ebola daga ƙasar waje ya shigo da ita Najeriya
Yadda Ebola ta shigo Najeriya
Kun ji cewa sababbin bayanai sun nuna cewa matar da aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola a Abuja ta shigo Najeriya ne a ranar 3 ga Oktoba, 2026.
Bayanai sun tabbatar da cewa an gano cewa ta shigo Najeriya ne ta jirgin saman Ethiopian Airlines a farkon wannan wata na Oktoba da muke ciki.
Asali: Legit.ng
