Hajjin Bana
Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya gwangwaje Alhazan jihar da kyautar Riyal 100 kowannensu a ƙasa mai tsarki. Gwamnan ya kuma ba ma'aikata Riyal 200.
Hukumar Alhazai a birnin Abuja, ta sanar da rasuwar daya daga cikin mahajjata mai suna Hajiya Amina Yunusa a birnin Makkah, ta mika sakon ta'aziya ga iyalanta.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ba wa alhazan jihar fiye da 3000 Riyal 300 don rage musu radadi, ya roke su da zuci gaba da yiwa jihar addu'a.
An hangi gwamnan jihar Bauchi, Sanat Bala Abdulkadir Mohammed yana jagorantar wasu Alhazai sallah a filin arfa. Hoton da gwamnan ya dora a shafinsa ya ja hanku.
Alhazan jihar Osun sun fusata kan rashin ingancin abincin da ake ciyar da su da shi a ƙasa mai tsarki. Alhazan sun gudanar da zanga-zanga domin nuna fushin su.
Hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) ta tabbatar da mutuwar alhazan kasar guda shida da ke aikin hajjji a kasar Saudiyya. Bibbiyu daga Kaduna da Osun, 1 a Filato.
Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta ce ta yi jigilar maniyyata 67,000 daga cikin 73,000 ta bangaren da aka ware, ta shawarci mutane kan tsarin ajiya nahukumar.
Akwai mutane da-dama da sun biya kudin aikin hajji, amma ba su makomarsu ba. NAHCON ta tabbatar da cewa babu wanda za a bari ba tare da ya sauke farali ba.
Yayin da aka sanar da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah, akwai bukatar Musulmai su kiyaye ranaku 3 da ke da muhimmanci a wannan wata mai alfarma da za a shiga.
Hajjin Bana
Samu kari