An Samu Matsala Bayan Hukumar Alhazai Ta Gaza Cike Yawan Kujerunta Dubu 95, an Fadi Babban Dalili

An Samu Matsala Bayan Hukumar Alhazai Ta Gaza Cike Yawan Kujerunta Dubu 95, an Fadi Babban Dalili

  • Da alamu yanayin tsadar kujerar hajji ya kawo cikas ga Hukumar Alhazai ta Kasa wurin cike gurbin kujerunta
  • Akalla yawan kujerun da aka ware wa hukumar dubu 95 ba za ta iya cike su ba a wannan shekara
  • Hausa Legit ta ji ta bakin wani Alhaji kan wannan matsala da hukumar ta samu game da aikin hajji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana damuwa kan matsalar rashin biyan kudaden aikin hajjin bana.

Akwai alamun cewa yawan kujerun da aka ware wa hukumar na dubu 95 ba za ta iya cike su ba a shekarar 2024.

Kara karanta wannan

"Mutane na zaman jira": Ango ya fasa aurensa yan awanni kafin biki, ko'ina ya hargitse

Hukumar NAHCON ta koka kan rashin biyan kudaden aikin hajji
Hukumar Alhazai Ta Gaza Cike Yawan Kujerunta Dubu 95 a Bana. Hoto: NAHCON.
Asali: Facebook

Yaushe za a rufe karbar kudaden hajji?

Hukumar ta sanya 31 ga watan Disamba a matsayin ranar karshe ta biyan kudaden a sassan hukumar ta jihohi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, hukumar ta sanya ranar ce don tabbatar da cewa ta samu yawan mutanen da za su sauke farali a wannan shekara.

Sannan tsarin zai taimaka wa hukumar wurin ganin ta fara shirye-shirye da hukumomin jigilar maniyya a Najeriya da kasar Saudiyya.

Sai dai tsadar kujerar da kuma sanya ranar rufe karbar kudaden ya sa yawan mutanen ya ragu sosoi fiye da yadda ake tsammani.

Duk da cewa hukumar ba ta sanar da cewa za ta kara wa’adin ba, Daily Trust ta tattaro cewa maniyyata ba su wuce dubu 25 ba ne suka biya.

Wasu matsaloli ake samu game da aikin hajjin bana?

Yanayin matsin tattalin arziki da ake ciki shi ma ya taka muhimmiyar rawa wurin matsalar yayin da kaso 99 cikin dari na kudaden ake biya da dala.

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya ta kama jami’inta kan mutuwar direban babban mota a Borno

A shekarar 2013 kudin kujerar hajji bai wuce naira 639,498 yayin aka kara a 2014 zuwa 689,061 sai kuma 723,76 a shekarar 2015.

Sai dai kudin kujerar ya karu zuwa 905,556 a 2016 yayin da a 2017 ya kai miliyan 1.4, sannan a 2020 ya kai miliyan 1.5, cewar Forefront.ng.

A wannan shekarar ta 2023 farashin ya kai miliyan uku inda ake hasashen zai iya karuwa zuwa miliyan biyar ko fiye saboda tsadar dala.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani Alhaji Ibrahim Muhammad Zubair wanda ya ziyarci dakin Allah shekaru biyu da suka wuce.

Ibrahim ya ce ya so ya koma wannan shekara amma saboda tsadar kudin kujera shi ne abin da ya kashe masa gwiwa.

Ya ce:

"Yanzu haka akwai abokina wanda ya daura aniyar zuwa a wannan shekara amma dole haka ya hakura bayan sanar da kudin kujerar."

Ya ce zai yi wahala a sake cike gurbin kujerun ganin yadda kullum kara kudin ake yi saboda matsalar dala.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta raba gardama kan sahihancin shugaban karamar hukuma, ta yi hukunci mai tsauri

An bayyana kudin aikin hajjin 2024

A wani labarin, Hukumar NAHCON ta sanar da kudin kujerar aikin hajjin bana ta shekarar 2024.

Hukumar ta bayyana haka a ranar 16 ga watan Nuwamba inda ta ce za a biya miliyan 4.5.

Asali: Legit.ng

Online view pixel