Hajjin 2024: An Bayyana Kudin da Maniyyata Ka iya Biya Domin Zuwa Saudiyya

Hajjin 2024: An Bayyana Kudin da Maniyyata Ka iya Biya Domin Zuwa Saudiyya

  • A duk shekara musulman duniya suna gudanar da aikin Hajji domin cika ɗaya daga cikin rukunnan addinin musulunci
  • A Najeriya, shirye-shiryen aikin Hajji na zuwa ne da kalubale da dama da suka hada da ƙarin kuɗin tafiya zuwa Saudiyya
  • Kamfanoni masu kula da yawon buɗe ido sun yi gargaɗin cewa kuɗin aikin Hajjin shekara mai zuwa na iya tashi sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Kano - Ƙungiyar kamfanoni masu kula aikin Hajji da Umrah na Najeriya (AHUON) ta koka kan yiwuwar tashin kuɗin zuwa aikin Hajji a shekarar 2024 da ke tafe.

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa tashin gwauron zaɓi da Dalar Amurka ke yi ne zai haddasa hakan.

Kudin aikin Hajji za su karu a 2024
Kungiyar AHUON ta ce akwai yiwuwar a samu karin kudin aikin Hajji a 2024 Hoto: Aminu Abubakar, Urbazon
Asali: Getty Images

Hajjin 2024: AHUON ta yi magana kan yiwuwar ƙarin kuɗi

Kara karanta wannan

Ndume da Lawal: Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sahihancin nasarar Sanatocin arewa 2

A cewar jaridar Vanguard, ƙungiyar AHUON ta bayyana cewa mahajjata masu niyyar zuwa aikin Hajji na iya biyan kusan N6m saɓanin N3m da aka biya a lokacin aikin Hajjin 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan tsokacin ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar AHUON na ƙasa Alhaji Yahya Nasidi, lokacin da yake jawabi a birnin Kano yayin taron wayar da kai kan aikin Hajjin 2024 a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamban 2023.

Nasidi ya nuna damuwarsa kan yadda kuɗin zuwa aikin hajjin 2024 zai ninka na shekarar 2023 saboda tashin gwauron zaɓi da Dalar Amurka ke yi, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

Wane taimako FG za ta bayar?

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) da su taimaka ta duk hanyar da za su iya domin shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da CoS na shugaban majalisar dokokin Adamawa, sun turo saƙo mai tada hankali

Ya buƙaci gwamnatin da hukumar NAHCON su taimaka musu wajen ajiye kuɗaɗensu a ƙasar Saudiyya.

Alhaji Nasidi ya bayyana cewa:

"Muna fargabar abin da zai faru idan gwamnati ba ta shiga cikin lamarin ba."
"A shekarar da ta wuce mun gudanar da aiki a kan N3m, yanzu zai iya wuce N6m domin haka ne muke kira ga masu son zuwa aikin Hajjin bana da su yi ƙoƙarin biyan kudin aikin Hajjinsu da cikin lokaci"
"Saboda idan ba a biya ba, ba za a iya samun biza ba, kuma ba za a iya tafiya ba."

Matashi Ya Samu Kujerar Aikin Hajji

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gwangwaje wani matashi da kyautar kujerar zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.

Dayyabu Haladu ya samu wannan kyautar ne bayan ya mayar da Dala dubu 16 da ya tsinta lokacin da ake gudanar da aikin Hajji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel