Sauke Farali Ya Kara Tsada, Gwamnatin Tinubu Ta Sanar da Kudin Kujerar Hajjin 2024

Sauke Farali Ya Kara Tsada, Gwamnatin Tinubu Ta Sanar da Kudin Kujerar Hajjin 2024

  • Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa Musulmai za su biya N4.5m a matsayin kuɗin kujerar hajji mai zuwa 2024
  • Hukumar kula da jin daɗin maniyyata (NAHCON) ce ta sanar da haka a wata sanarwa, ta kuma sanya wa'adin biyan kuɗin
  • Ta kuma shawarci Musulman da ke da niyyar zuwa sauke farali a shekara mai zuwa su biya kuɗin a kan lokaci domin samun gurbi da wuri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya ta sanar da cewa maniyyata za su biya Naira 4.5m kan kowace kujerar hajji ɗaya domin aikin Hajji mai zuwa na shekarar 2024.

NAHCON ta sanar da kuɗin hajjin bana.
Sauke Farali Ya Kara Tsada, Gwamnatin Tinubu Ta Sanar da Kudin Kujerar Hajjin 2024 Hoto: Haramain Sharifain
Asali: Twitter

Hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa (NAHCON) ce ta bayyana sabon farashin kujerar aikin hajjin ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Tinubu ya shiga babbar matsala kan tsige Gwamna Abba Gida-Gida

NAHCON ta wallafa sanarwa a shafinta na Facebook cewa Musulmai masu niyyar sauke farali a 2024, za su biya Naira miliyan 4.5 a matsayin kuɗin hajji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jadawalin biyan kudin hajjin 2024

Haka nan kuma hukumar ta fitar da wa’adin biyan kudin hajji ga masu niyya, inda za’a tura kudaden a cikin kwanaki 50 daga ranar da aka sanar da fara biyan kuɗin hajji.

Ta kuma kayyade cewa za a rufe bayar da biza cikin kwanaki 165 daga wannan rana da ta sanar da kuɗin kujera, kwanaki 212 kafin hawan Arfah.

Ana shawartar maniyyata aikin Hajji da su biya kuɗin a kan lokaci domin su samu gurbi da wuri-wuri kafin wa'adin da NAHCON ta gindaya ya cika.

Aikin hajji na ɗaya daga cikin ginshiƙai biyar waɗanda Addinin Musulunci ya ginu a kansu, sai dai rukunin na zama wajibi ne ga wanda Allah ya baiwa dama.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan Majalisa ɗaya tilo da take da shi a jihar Arewa, ya koma APC

Legit Hausa ta tattauna da wasu Musulmai kan wannan ƙarin kuɗi, sai dai a cewarsu hakan ba zai hana zuwa aikin hajji ba.

Wani mai suna Auwal Ahmad, wanda ake ce wa Malam Auwal ya ce a zahirin gaskiya Gwamnatin Najeriya ba ta wani yunƙuri na ganin tsadar rayuwar nan ta ragu.

A cewarsa, idan akwai inda ya kamata a saka tallafi to aikin hajji na ɗaya daga ciki domin ɗaya ne daga cikin rukunan Musulunci.

Ya ce:

"Wannan ƙarin ba zai hana Mutane zuwa Hajji ba, sai dai ni a tunani na, ya kamata nan aka sa mana tallafi. Hajji na ɗaya daga cikin rukunan Musulunci."
"Komai ƙara tsada yake a Najeriya, farashin yau daban na gobe daban. ban ga abin da shugabanni ke yi kan haka ba."

A nasa martanin, Kabir Sa'idu, ya faɗa wa wakilinmu cewa shi ya daina sa ran wani abu sai sauko a ƙasar nan, amma batun hajji ko nawa zai kai duk wanda Allah ya kira zai tafi in ji shi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban Malami a arewa, sun kashe shi bayan karɓan kuɗin fansa

Kauran Bauchi ya yaba da hukuncin Kotun ɗaukaka kara

A wani rahoton na daban Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, ya maida martani bayan Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar da ya samu

Kauran Bauchi ya yaba da hukuncin wanda ya ƙara tabbatar da sahihancin zaɓen da ya lashe ranar 18 ga watan Maris

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel