Fulani Makiyaya
Rundunar sojin Najeriya ta gargadi Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho kan irin kalaman da ya ke yi tun bayan dawowa Najeriya a ranar 22 ga watan Faburairu.
Dan fafutukar kasar Yarabawa, Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce ba gudu ba ja da bayan wajen kare 'yancin kasar Yarabawa.
Harkokin kasuwanci sun tsaya caka Legas yayin da wani mutum ya rasa ransa da wasu suka jikkata bayan an kare tsakanin Hausawa da Yarbawa a jihar.
Majalisar tsaro ta jihar Benuwe ta baiwa makiyaya wa'adin kwanaki 14 da su daina kiwon dabbobi a fili ko kuma su fuskanci hukunci kamar yadda dokar jihar ta tanadar.
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani kwamitin aiwatar da shirin na ‘Pulaku’, da nufin magance matsalolin rikicin manoma da makiyaya da kuma samar da hadin kan kasa.
Majalisar jihar Oyo ta bukaci cafke shugaban Fulani, Seriki Chumo kan zargin kisan manomi da jami'in tsaron Amotekun a yankin Iwajowa da ke jihar.
Wasu makiyaya uku da ake zargi da kisan wani fasto mai suna Segun Adegboyega a yankin Ogbomoso, jihar Oyo sun shiga hannu. Suna tsare a ofishin ‘yan sandan Owode.
Za a ji yadda mace ta haihu a tsakiyar jama’a yayin da aka hallaka mazaje a kashe-kashen Filato. Akwai wanda take shirin aurar da yaronta da ta rasa komai a duniya.
Sababbin bayanai sun fito bayan bacewar shugaban 'yan Miyetti Allah Kautal Hore a Nasarawa. Hukumar DSS tace ba ta tsare da shugaban kungiyar makiyayan.
Fulani Makiyaya
Samu kari