Bayan Zargin Miyetti Allah Kan Gwamna Sule, an Dauki Mataki Kan Ƙungiyoyin Sa Kai

Bayan Zargin Miyetti Allah Kan Gwamna Sule, an Dauki Mataki Kan Ƙungiyoyin Sa Kai

  • Yayin da ake tababa kan kungiyoyin sa-kai na kabilanci a jihar Nasarawa, Gwamna Sule Abdullahi ya dauki mataki kansu
  • Gwamnan ya sanar da haramta dukkan ayyukan kungiyoyin tare da umartansu da mika makamai ga kwamishinan 'yan sanda
  • Hakan bai rasa nasaba da zargin da shugaban Miyetti Allah ya yi kan jagorantar ƙungiyar zaman lafiya a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya rusa dukkan kungiyoyin sa kai na kabilanci.

Hakan ya biyo bayan ganawar gaggawa da ya shafi tsaro da aka yi a jihar yayin da ake fama da matsalar tsaro.

Gwamna ya haramta kungiyoyin sa kai bayan zargin Miyetti Allah
Gwamna Sule ya haramta kungiyoyin sa-kai bayan zargin Miyetti Allah. Hoto: Bello Badejo, Abdullahi Sule.
Asali: Facebook

Wane umarni Gwamna Sule ya bayar?

Kara karanta wannan

Al'ummar Kano sun nuna fargaba kan yadda shari'ar Ganduje zata kawo rikici a jihar

Channels TV ta tattaro cewa gwamnan ya umarci dukkan kungiyoyin da dokar ta shafa su dawo da makamai da kayansu ga kwamishinan 'yan sanda a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya ce ya dauki matakin ne bayan shawarar da kwamitin tsaro ya bayar dangane da kungiyoyin.

Kungiyoyin da abin ya shafa sun hada da kungiyar zaman lafiya ta Fulani da 'yan sa kai na Bassa da kuma Eggon, a cewar rahoton Daily Post.

Har ila yau, gwamnan ya haramta dukkan wasu kungiyoyi ko taron al'umma da ke da alaka da kungiyoyin sa kai na kabilanci a jihar.

...Ya haramta kungiyoyin sa kai na kabilanci

"Kungiyar zaman lafiya na Fulani da 'yan sa kai na Bassa da na kabilar Eggon dukkansu an haramta su."
"An kuma ayyana su a matsayin haramtattun kungiyoyi da ke kawo cikas ga ci gaban wannan jiha."

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya dauki zafi bayan sakin 'yan daba daga kulle, ya sha alwashi kan lamarin

- Sule Abdullahi

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin kungiyoyin da wuce gona da iri a harkokin tsaron jihar.

Shugaban Miyetti Allah ya zargi Gwamna Sule

A baya, kun ji cewa shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Badejo ya zargi Gwamna Sule Abdullahi na jihar Nasarawa kan tilasta shi jagorantar kungiyar sa-kai.

Badejo ya ce gwamnan ne ya shawarce shi da ya jagoranci kungiyar zaman lafiya domin dakile matsalar rashin tsaro a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan cafke Badejo kan zargin ta'addanci da hukumar DSS ta yi a farkon wannan shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel