Wahalar man fetur a Najeriya
Masu sayar da fetur a bayan fage da aka fi sani da 'yan bumburutu sun fara sayar da lita 1 akan naira 1,000 yayin da aka fara wahalar mai a Legas, Abuja da Ogun.
Kungiyar masu motocin haya ta Najeriya (NARTO), ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar biyo bayan ganawar da suka yi da gwamnatin tarayya.
Wani mutum ya nuna kaduwarsa kan farashin da ya siya man fetur a jihar Enugu. Mutumin ya nuna shaida sannan ya bayyana sunan gidan man da ya siye shi kan haka.
Matakin dakatar da ayyuka manyan tankokin dakon man fetur da ƙungiyar NARTO ta ɗauka ya haddasa dogon layi da ƙarancin kan fetur a birnin tarayya Abuja.
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma lauya, Cheif Reuben Famuyibo, ya gargadi shugabannin Arewa da su daina cusa ƙiyayyar Shugaba Tinubu a zukatan 'yan Najeriya.
Dillalan hatsi a kasuwar hatsi ta kasa da kasa ta Dawanau a jihar Kano sun karya farashin hatsi domin rage radadin da jama'a ke fuskanta a jihar.
Hukumar da ke sa ido kan man fetur da iskar gas a Najeriya (NUPRC) za ta mayar da wasu sassan ta zuwa Legas daga Abuja, hakan zai shafi sama da ma’aikata 200.
Najeriya ta cigaba da biyan tallafin da Tinubu ya cire a kan man fetur a halin yanzu. IMF ta zargi Gwamnatin tarayya da biyan kudi domin hana fetur tashi.
Man fetur yana cigaba da kara tsada a lokacin da rayuwa ta ke kara kunci. Har zuwa yanzu akwai fetur a Abuja, masu motoci suna shan lita ne a kan N675/l.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari