Adeleke Ya Amince da Biyan N15,000 Ga Ma’aikatan Jihar Osun, ’Yan Fansho Sun Samu N10,000

Adeleke Ya Amince da Biyan N15,000 Ga Ma’aikatan Jihar Osun, ’Yan Fansho Sun Samu N10,000

  • Gwamnatin jihar Osun ta sanar da fara biyan ma'aikatan jihar naira dubu goma sha biyar yayin da 'yan fansho za su samu naira dubu goma
  • Wannan tallafi ne da Gwamna Adeleke na jihar ya amince a biya ma'aikata da 'yan fanshon don rage radadin cire tallafin mai
  • Tallafin wanda za a rinka biyan ma'aikata da 'yan fansho a kowanne wata, zai gudana na tsawon watanni biyu, za a fara daga watan Disamba 2023

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya amince da biyan naira dubu goma sha biyar duk wata matsayin alawus ga ma'aikatan gwamnati a jihar a don rage radadin cire tallafin mai.

Kara karanta wannan

Bidiyon zanga-zangar da ta barke a Kano kan zargin 'yan sanda sun kashe farar hula

Gwamnan ya kuma amince da bayar da tallafin naira dubu goma duk wata ga ‘yan fansho domin rage wahalhalun da suke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur.

Gwamna Adeleke/Jihar Osun
Domin rage radadin cire tallafin man fetur, Gwamna Adeleke zai rika biyan ma'aikatan jihar N15,000 kowanne wata. Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Yarjejeniya tsakanin Gwamna Adeleke da kungiyar kwadago

Sakataren ma'aikatar kula da bunkasa ma'aikata na jihar ya fitar da takardar da ke dauke da umurnin Gwamna Adeleke, wacce aka fitar a ranar 28 ga Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardar wacce aka aikewa duk shuwagabannin hukumomi da ma'aikatun jihar an yi mata take da "Tabbatar da fara biyan tallafi ga ma'aikatan gwamnati da 'yan fansho na jihar Osun."

Wannan matakin ya biyo bayan tattaunawa da kuma cimma yarjejeniya da aka yi tsakanin Adeleke da shugabannin kwadago na jihar, The Nation ta ruwaito.

Yaushe gwamnati za ta fara bayar da tallafin?

A cewar takardar:

"Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke, ya amince da biyan naira dubu sha biyar ga kowanne ma'aikaci da kuma naira dubu goma ga kowanne dan fansho a jihar Osun.

Kara karanta wannan

Yan fansho ga Tinubu: Cire tallafin mai ya jefa mu cikin mawuyacin hali

"Kudaden wadanda za a rinka biya kowanne wata, za su taimaka wajen rage radadin da mutane suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi."

Legit ta ruwaito cewa sanarwar ta yi nuni kan za a fara biyan kudin ne daga watan Disamba 2023, kuma za a rinka biya na tsawon watanni shida.

Gwamnatin jihar na fatan wannan tallafi ya taimaka wajen karawa ma'aikatan jihar hazaka wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Ado Doguwa ya zargi NNPP da aringizon kuri'u a zaben Kano

A wani labarin daga Legit Hausa, dan majalisar mazabar Tudun Wada/Doguwa ya zargi jam'iyyar NNPP ta tafka magudi a zaben gwamnan jihar da ya gudana a 2023.

Ahassan Ado Doguwa ya ce NNPP ta yi amfani da kuri'un bogi wajen yin aringizon kuri'u wanda ya ba jam'iyyar nasara a zaben 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel