Da Kamar Wuya: Zai Yi Wahala Matatun Najeriya Su Yi Aiki Inji Tsohon Shugaban NNPC

Da Kamar Wuya: Zai Yi Wahala Matatun Najeriya Su Yi Aiki Inji Tsohon Shugaban NNPC

  • Alex Ogedengbe ya sacewa mutane kwarin gwiwarsu a kan matatun man gwamnati da ya bayyana ra’ayinsa
  • Tsohon shugaban kamfanin na NNPC yana ganin zai yi wahala matatar Fatakwal ta dawo aiki a Disamban nan
  • Ko da an iya farfado da matatun Fatakwal da na Kaduna, Alex Ogedengbe ya ce ba za a samu wani fetur sosai ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A wata zantawa da aka yi da shi, Alex Ogedengbe wanda ya taba rike kamfanin NNPC, ya ce zai yi wahala matatu su fara aiki.

Mista Alex Ogedengbe yana ganin da kyar matatar man Fatakwal ta iya fara tace danyen mai a shekarar nan, This Day ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Ba yau ne farau ba: Kwankwaso ya yi tir da Sojojin da su ka kashe mutane a Kaduna

NNPCL.
Shugaban kamfanin NNPCL Hoto: transportday.com
Asali: UGC

Lafiyar matatun kamfanin NNPCL

A ra’ayin Alex Ogedengbe, ba dole ba ne matatar da ake jira ta soma aiki a Disamba kamar yadda kamfanin NNPCL ya sanar da duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ko da matatun Fatakwal da Kaduna sun koma aiki, tsohon shugaban kamfanin man ya ce bai fi su samar da 25% na fetur da ake bukata ba.

Za a samu fetur a Najeriya?

NNPCL ya yi alkawarin idan matatun sun fara tace mai, za a iya samun gangunan fetur 60, 000, watakila hakan ya rage farashin litar mai.

A hirar da aka yi da shi a gidan talabijin Channels, Ogedengbe ya ce bidiyon da ya gani ya nuna ba zai yiwu a tace mai a watan nan ba.

Tsohon shugaban kamfanin na NNPC yake cewa matatun da ake kokarin gyarawa, sun shafe tsawon shekaru 30 ba tare da sun yi aiki ba.

Kara karanta wannan

"Zai shafe watanni 4:" Kotu ta tura wani matashi magarkama saboda satar doya a Abuja

A cewarsa, an tanadi 98% na kayan da ake bukata, amma har yanzu bai wuce 75% na daukacin aikin farfado da matatar Fatawal aka yi ba.

Matatun fetur za su tashi a Disamba?

"Zuwa karshen Disamba, idan an yi kokari shi ne a kammala shirye-shirye, daga nan sai su fara gwajin dukkanin kaya da na’urori.
Za ayi gwajin na’urori a ga yadda za su yi aiki. Daga nan sai a hada komai tare. Gwajin zai iya daukar makonni biyu zuwa wata."

- Alex Ogedengbe

Tun 1990 rabon da matatun su tace mai, sai yanzu ake ta kokarin ayi gyare-gyare amma Injiniyan ya ce matatun duk sun tsufa sosai.

Peter Obi & Gwamnatin Tinubu

Rahoto ya zo cewa ana neman N15bn a gyara gidan mataimakin shugaban kasa, Peter Obi ya ce kudin zai biya albashin Farfesoshi 3000.

Sannan Obi ya yi Allah-wadai da kudin da aka kashe da Bola Tinubu ya dauki mutane zuwa taron COP28, hakan ya jawo masa raddi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel