Gobara
Rahotanni sun bayyana cewa masu shagunan ɗinki a wata kasuwar zamani da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa sun yi asarar kayan miliyoyin Naira.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gobara ta kama a ofishin hukumar NSIPA inda ta yi sanadin lalacewar abubuwa a ma'ajiyar ciki har da kayan horaswa na N-Power.
Mataimakin gwamnan Borno, Dr. Usman Kadafur ya tsallake rijiya da baya. Jirgin Max Air da ya dauko shi da wasu fasinjoji 70 ya samu matsalar inji.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta bayyana irin barnar da gobara ta yi a cikin watan Nuwamban 2024. Hukumar ta ce gobara ta lalata kayayyakin miliyoyin Naira
Mummunar gobara ta yi barna a jihohin Yobe, Kwara, da Taraba, inda ta kone shaguna da wuraren hutu tare da haddasa asarar dukiyoyi masu tarin daraja.
Wata gobara da ta tashi a ofishin hukumar zabe ta INEC a Delta, ta lalata kayayyaki. Lamarin ya auku ne a daya daga cikin ofisoshin hukumar na kananan hukumomin
wata gobara da ta kama sakamakon haɗuwar motar katifa da wayar wutar lantarki ta babbake kayan maƙudan kudi a wata kasuwa a Ilorin a jihar Kwara.
'Yan kasuwa sun gamu da jarrabawa a Yobe. An wayi gari da mummunan iftila'in gobara. Hukumar SEMA ta jihar ta sanar da Legit adadin asarar da aka tafka.
An samu tashin gobara a cikin daren ranar Lahadi a babban birnin tarayya Abuja. Gobarar dai ta tashi a kasuwar da ke cikin rukunin gidajen Trademore.
Gobara
Samu kari