Yaki da ta'addanci a Najeriya
A labarin nan, za a ji cewa rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta bayyana abubuwan da suka jawo tsaiko wajen shari'ar yan ta'addan Ansaru da ke hannun hukuma.
Akwa Ibom ta dakatar da Sarkin Ikot Umo Essien saboda zargin ta’addanci da lalata kasuwa; gwamnati ta kuma karyata jita-jitar janye tsaron tsohon gwamna.
A labarin nan, za a ji yadda gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa tana kokarin kawo zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da amfani da karfin bindiga ba.
Gwamnatin Najeriya ta warware wasu abubuwa da Donald Trump ya fada game da kasar a taro da jakadun kasashen waje a Abuja. An yi taron a Abuja ranar Laraba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun shiga kauyen Doguwar Dorawa a karamar hukumar Bakori, jihar Katsina, sun yi wa mutum 2 yankar rago.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna farin cikinsa bisa yadda jami'an tsaro suka tari yan bindiga lokacin da suka kai hari a yankin Shanono.
Sojojin Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan Boko Haram shida a Mallam Fatori, sun kwato bindigogi, jirage marasa matuka, da makamai yayin da suka dakile hari.
A labarin nan, za a ji cewa kungiyar raya kasashen Afrika ta Yamma ta bayyana matsayarta a kan zargin cewa ana kisan kare dangi a kan kiristocin Najeriya.
Jami'an tsaron CPG na gwamnatin jihar Zamfara sun samu nasarar kama wata mota dauke da bindigogi da alburusai a kauyen Dangulbi, an fara bincike kansu.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari