Yaki da ta'addanci a Najeriya
Tsagerun 'yan bindiga sun yi ajalin rayuka huɗu yayin da suka kai hari karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, an ce sun shiga har fadar sarkin Maru, Abubakar Maigari.
Nnamdi Kanu zai tashi da N8bn daga hannun Gwamnatin Tarayya tun da IPOB ta yi galaba a Kotu. Alkali ya ce tsare shi da ake ta yi ya saba doka da tsarin mulki.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda, ya ce ko alama ba zai nemi tattauna wa da yan bindigan daji ba, maimakon haka zai yaƙe su da karfin soji sai sun tuba da kansu.
Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun yi ajalin wasu yan gudun hijira da suka baro sansanin zasu je kamun kifi a karamar hukumar Gwer ta yamma a Benue.
Ana da labari wasu hare-hare da aka kai a a Birnin Gwari, an kashe mutane akalla hudu a jihar Kaduna, inda aka kai hare-haren ba su da nisa da sojojin kasa.
Tsagerun 'yan bindiga sun halaka jami'in rundunar mafarauta yayin da suka fita sintiri a kan titin Birnin Gwari, sun kuma kashe direbobin motocin haya biyu.
Sojojin kungiyar Ansaru sun fara fitowa karara a gabashin Birnin gwari. ‘Yan ta’adda sun fara fitowa daga jeji, su na auren 'yan matan mutanen gari.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kan wani Masallaci a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, sun halaka Liman da wani masallaci ɗaya ranar Talata.
Dakarun tsaron haɗin guiwa sun shiga cikin daji sun farwa yan bindigan daji a jihar Kebbi, sun samu nasarar kashe ɗaya kuma suka ceto mutane uku.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari