Kotu Ta Soke Haramcin da Aka Yi wa ‘Yan IPOB, Za a Biya Nnamdi Kanu Diyyar N8bn

Kotu Ta Soke Haramcin da Aka Yi wa ‘Yan IPOB, Za a Biya Nnamdi Kanu Diyyar N8bn

  • Babban Kotun jihar Enugu ta ruguza matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na haramta aikin ‘yan kungiyar IPOB
  • Alkali A. O. Onovo ya yi hukunci cewa ba za a iya makawa kungiyar jan fenti ba saboda ta na neman ‘yancin-kai a kasa
  • A sakamakon gaskiyar da Alkali ya ba Nnamdi Kanu, shugaban na IPOB zai tashi da N8bn daga hannun gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Enugu - Alkalin Babban Kotun jihar Enugu, A. O. Onovo ya zartar da cewa haramta aikin kungiyar IPOB da aka yi a baya ya saba doka.

Punch ta ce A. O. Onovo ya yi hukunci cewa matakin da aka dauka na ayyana IPOB a matsayin haramtacciyar kungiya ba daidai ba ne.

Mai shari’a Onovo ya ce hakan ya saba doka kuma ya ci karo da kundin tsarin mulki, saboda haka ya rusa matakin da aka dauka a 2017.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

IPOB.
Magoya bayan IPOB da Nnamdi Kanu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An jefa IPOB cikin 'yan ta'adda a Najeriya

Gwamnonin Kudu maso gabas a karkashin jagorancin David Umahi su ka fara hana aikin kungiyar, sai gwamnatin tarayya ta bi sahu.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin ‘yan ta’adda.

Kanu ya yi nasara a kan Gwamnati a kotu

Amma da aka je kotu, lauyan jagoran na IPOB, Nnamdi Kanu mai suna Aloy Ejimakor, ya nemi a soke wannan tambari da aka daura masu.

Channels ta ce Barista Ejimakor ya yi ikirarin ba a bi doka wajen bin wannan mataki ba domin su na bin hanyar siyasa ne wajen neman ‘yanci.

Lauyan ya fadawa kotu cewa a cikinsu akwai Ibo da sauran kabilun Kudu maso gabas.

Za a biya shugaban IPOB N8bn

Baya ga haka, Nnamdi Kanu ya roki kotun ta ayyana cafke shi da aka yi da tsare shi da ake cigaba da ya yi a matsayin wanda ya saba doka.

Kara karanta wannan

Mutane 2 kaɗai Su ka fi Ni Yi wa Tinubu Kokari,Na Cancanci Kujerun Ministoci – Rarara

Kanu wanda ya dade a tsare ya na ikirarin cewa an ci zarafinsa a kundin tsarin mulki.

Onovo ya gamsu cewa babu dalilin daure wanda ya ke fafutukar neman ‘yanci, a dalilin haka ya ce a biya shi kudi kuma a nemi afuwarsa.

Baya ga afuwarsa da za a nema a gidajen jaridu, Alkalin ya ce za a biya wanda ya yi kara N8bn saboda mummunan halin da aka jefa shi a ciki.

An fito da shugaban IPOB?

Ana yawo da rade-radi cewa hukumar DSS ta saki shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, amma a zahirin gaskiya ba haka lamarin yake ba.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa babu gaskiya a batun sakin Kanu. Rahoto ya zo cewa DSS na cigaba da tsare shi duk da ya samu beli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel