Aikin Gwamnatin Najeriya
Bola Tinubu ya nada mutane 10 da za su jagoranci MOFI. Dr. Shamsudeen Usman ya zama Shugaban majalisar sa ido shi kuma Dr. Armstrong Ume Takang shi ne CEO.
Gwamnatin jihar Kano ta gano wasu daliban makarantar sakandire (JSS da SSS) a cikin ma'aikatan jihar. An kuma gano masu bautar kasa da dan shekara 13 a ciki.
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta kaddamar da wani shiri na bayar da bashin naira dubu hamsin ga kanan da matsakaitan 'yan kasuwa har mutum miliyan 1.5.
Yanzu babu abin da Bola Tinubu yake so kamar a ce an sa sunansa a cikin littafin nan na Guinness. Tinubu yana so ya bi sahun Hilda Baci da Hadimin magajinsa.
Za a ji yadda ‘Yan siyasa ke ta sintiri a Aso Rock domin zama Jakadu zuwa kasashen waje. An ba Bola Tinubu shawarar wadanda ya kamata su zama Jakadun Najeriya.
Hukumar Inshorar masu ajiyar kudi ta Najeriya (NDIC), ta ce nan ba da dadewa ba, za ta biya karin naira biliyan 16.16 ga kwastomomin bankuna 20 da suka rushe.
Kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC, sun umurci mambobinsu da su fara yajin aiki a fadin kasar, sakamakon harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.
Ofishin jakadancin Kanada a Najeriya ya ce ya dakatar da ayyukansa a kasar saboda matsalar tsaro. A ranar Litinin ne wani sashe na ofishin ya kama da wuta.
Hukumar NEITI ta ce daga shekarar 2017 zuwa 2021, barayi sun sace ganguna fiye da miliyan 200 na arzikin danyen mai, an jawowa Najeriya asarar Naira Tiriyan 4.3
Aikin Gwamnatin Najeriya
Samu kari