Tinubu Ya Amince Da Biyan Makudan Kudaden Alawus N25,000 Ga Likitoci

Tinubu Ya Amince Da Biyan Makudan Kudaden Alawus N25,000 Ga Likitoci

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta amince da biyan alawus na N25,000 ga likitoci da sauran ma'aikantan lafiya na Gwamnatin Tarayya
  • Shugaban hukumar kula da albashi da alawus ta kasa, Ekpo Nta ya tabbatar da amincewar shugaban akan biyan kudaden a Abuja
  • Wannan sanarwa ta Gwamnatin Tarayyar na zuwa ne bayan likitocin sun shiga yajin aiki saboda rashin cika musu alkawura daga gwamnatin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan alawus na makudan kudade har N25,000 ga likitoci da sauran ma'aikantan lafiya na Tarayya.

Wannan amincewar na zuwa ne bayan likitocin sun shiga yajin aiki saboda rashin daidaito a tsakaninsu da Gwamnatin Tarayya.

Tinubu ya biya kudaden alawus N25,000 ga likitoci kan yajin aiki
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Ya Amince Da Biyan Makudan Kudaden Alawus N25,000 Ga Likitoci Kan Yajin Aiki. PM News.
Asali: Twitter

Shugaban hukumar kula da albashi na Tarayya, Ekpo Nta ya tabbatar da amincewar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu akan biyan kudaden a Abuja.

Kara karanta wannan

Majiyoyi Sun Bayyana Wanda Tinubu Zai Iya Nadawa a Matsayin Ministan Lafiya Yayin da Ya Mika Sunayensu Majalisa

Gwamnatin Tarayya ta kuma yi cikakken bayani akan wasu daga cikin matsalolin likitocin da ya jawo yajin aikin, PM News ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Likitoci sun shiga yajin aiki ne saboda gaza biya musu bukatunsu

Likitocin dai sun shiga yajin aikin ne bayan korafin da suka ta yiwa Gwamnatin Tarayya ba tare da biya musu bukatunsu ba.

Kungiyoyi da dama na barazanar shiga yajin aikin saboda wasu matsalolin su na daban da suke nema a wurin gwamnatin, cewar BusinessDay.

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi barazanar shiga yajin aiki a watan Agusta kan karin albashin ma'aikata tun bayan cire tallafin mai a kasar.

Kungiyar na ci gaba da tattaunawa da gwamnatin akan matsaloli da suka shafi cire tallafin da kuma karin albashi.

Gwamnatin Tarayya ta kuma yi bayanin kudaden alawus na hatsari da aka ware

Kara karanta wannan

An Samu Gwamnan APC Ya Yi Magana Game da Ministocin da Tinubu Ya Dauko

Ta kuma bayyana sauye-sauye na karin kashi 25 a CONMESS mataki 1-6 da kuma kashi 25 a CONMESS mataki na bakwai.

Sannan kuma kashi 25 a CONMESS 1-4 da kuma kashi 35 a CONHESS 15, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma yi bayanin alawus na hatsari ga likitocin da ke aiki a wajen asibiti.

Yajin Aikin Likitoci Ya Janyo Rasa Ran Mace Mai Juna Biyu Da Jaririnta

A wani labarin, wata mata ta rasa ranta sakamakon yajin aikin likitoci a kasar a jihar Nasarawa.

Matar ta rasa ranta ne da jaririnta sakamakon haihuwa a asibitin Dalhatu mallakin jihar Nasarawa.

An tabbatar cewa matar ta mutu ne sakamakon rashin likitocin da za su duba ta, wanda suke yajin aiki a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel