Bidiyon Gwaman PDP Yana Kamfe da ‘Shinkafa, Maggi’ a Arewacin Najeriya Ya Bayyana

Bidiyon Gwaman PDP Yana Kamfe da ‘Shinkafa, Maggi’ a Arewacin Najeriya Ya Bayyana

  • Darius Ishaku yana sa ran mutanen mazabarsa su zabe shi ya tafi majalisar dattawa a ranar Asabar
  • Da Gwamnan na Taraba ya ziyarci mutanensa, an ji shi a bidiyo yana kamfe da shinkafa da maggi
  • Ishaku yana tinkaho da cewa idan al’ummarsa suka ci, su ka koshi, to za su ba shi kuri’arsa a PDP

Taraba - Wani bidiyo ya bayyana a dandalin sada zumunta na Twitter, inda aka ji Darius Ishaku yana kamfe a wani yanki na jihar Taraba.

Legit.ng Hausa ba ta iya tantance a ina aka dauki bidiyon amma, amma an ji Gwamna Darius Ishaku yana jawabi mai kama da kamfe.

Fiye da mutum 80, 000 suka kalli wannan bidiyo da wani Shehu Abdullahi ya daura a shafinsa na @ShehunGwandu a yammacin ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Amurka Ya Aikowa 'Yan Najeriya da Sako Za a Shiga Filin Zabe

A bidiyon za a ji Gwamnan Taraba, Ishaku yana bayanin yadda zai rabawa mata kayan abinci domin su zabe shi a ranar Asabar mai zuwa.

Abin da Gwamna Ishaku ya fadawa mazabarsa

“Mata albishirinku, Na zo da maggi, na zo da shinkafa, shi za ku dafa ranar sati (Asabar), ku ci, ku ba mazajenku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Su ci, ku ba su kunu su sha, su je suyi layi, ku na bayansu, sai sun dangwala mana, sai sun dangwala mana...”

- Darius Ishaku

Bidiyon Gwaman PDP
Darius Ishaku da tukunyar shinkafa Hoto: guardian.ng da artsandculture.google.com
Asali: UGC

Wani matashi Kelvin Odanz ya caccaki Gwamnan na jihar Taraba bayan ganin bidiyon.

Odanz ya ce Ishaku yana cikin ‘yan siyasar da yake jin haushin su, ya zarge shi da girman kai, rashin iya aiki, raini da rashin koshin lafiya.

Wanene Darius Ishaku?

Mai girma Darius Ishaku yana neman takarar kujerar Sanatan kudancin jihar Taraba a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Ya Munana, Gwamnan Arewa Ya Shirya Yafe Takararsa Saboda a Doke Atiku

Kafin zamansa Gwamna a 2015, Ishaku mai shekara 68 ya rike kujerar Minista a lokacin Shugaba Goodluck Jonathan yana kan mulki.

Gwamnan ya na da burin maye gurbin Emmanuel Bwacha wanda shi kuma ya sauya-sheka zuwa APC, yana neman kujerar Gwamnan.

A gefe guda, mataimakin Gwamnan Taraba mai-ci, Haruna Manu yana neman zama Sanatan Taraba ta tsakiya a majalisar dattawa a PDP.

Dabarar da aka kawo - EFCC

A wani rahoto, kun ji cewa Hukumar EFCC ta ce gudun a saye kuri’un talakawa a zabe mai zuwa ne ya jawo aka canza takardun kudi.

Abdulrasheed Bawa ya ce sun samu bayanan sirri cewa mutane sun sayo kayayyaki da su raba a maimakon kudin da aka saba ba jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel