Hukumar INEC Ta Bayyana Adadin Masu Kaɗa Ƙuri'a a Zaɓen 2023
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana adadin yawan mutanen da suka karɓi katin zaɓen su
- A ranar Asabar mai zuwa ne dai za a fafata zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya a Najeriya
- Jihohin Legas da Kano sune ke a kan gaba wajen yawan masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya
Abuja- A yayin da ake shirin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya a ranar Asabar, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana adadin yawan ƴan Najeriyan da suka cancanci kaɗa ƙuri'a.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana dadin yawan mutanen da suka karɓi katin zaɓen su na din-din-din a matsayin 87,209,007. Rahoton Tribune
Shugaban ya bayyana cewa yawan adadin katin zaɓe na din-din-din 6,259,229 shine ba a karɓa ba ya zuwa ranar 5 ga watan Fabrairun 2023. Rahoton Daily Trust
A watan Janairun da ya gabata shugaban hukumar ya bayyana adadin yawan waɗanda suka yi rajista a matsayin 93,469,008.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jihohin Legas, Kano, Kaduna da Rivers sune suka fi ko waɗanne jihohi yawan waɗanda suka yi rajista.
Jihar Legas itace ta zo ta ɗaya da yawan waɗanda suka karɓi katin zaɓen su a matsayin 6,214,970 sannan jihar Kano ta zo ta biyu da 5,594,193. Jihohin Kaduna da Katsina suka zo na uku da na huɗu inda kowaccen su ke da 4,164, 473 da 3,459, 945.
Haka kuma yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma sune har yanzu ke da mafi yawan masu kaɗa ƙuri'a inda suke da 21,445,000 da 15,536, 213.
Yankin Arewa ta tsakiya yana 14,603,621, yankin Arewa maso Gabas yana da 11,937,769. Yankin Kudu maso Gabas yana da 10,401,484 yayin da yankin Kudu maso Kudu yake da 13,284,920.
A wani labarin kuma, an bayyana abinda ka iya janyowa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP rashin nasara a zaɓen ranar Asabar.
Atiku Abubakar shine ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng