Jihohin Da Manyan Ƴan Takara 4 Zasu Lashe Babu Tantama a Zaɓen 2023

Jihohin Da Manyan Ƴan Takara 4 Zasu Lashe Babu Tantama a Zaɓen 2023

  • Njeriya na dab da gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa a faɗin ƙasar wanda aka daɗe ana jiran zuwan sa
  • Akwai manyan ƴan takara hudu da ake yiwa kallon sune waɗanda za su iya yin nasara a zaɓen
  • Waɗannan ƴan takarar dai sun fito daga sassa daban-daban na ƙasar inda suke neman jan ragamar mulkin ƙasar nan

A ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun 2023, za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya.

Ƴan takarar shugaban ƙasa 18 ne dai za su fafata a zaɓen mai zuwa a ƙarƙashin jam'iyyun su.

Sai dai daga cikin ƴan takarar ana ganin gudu huɗu ne kawai daga cikin su ne kawai suke da yiwuwar yin nasara a zaɓen.

Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi na jam'iyyun PDP, APC, NNPP da LP sune ƴan takarar da ake yiwa kallon ɗaya daga cikin su ka iya yin nasara a zaɓen na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

"Na Sama Da Mu Sun Karbi Tuhumar", 'Yan Sanda Sun Bayyana Halin Da Ake Ciki Game Da Shari'ar Ado Doguwa

Legit.ng Hausa tayi nazari da duba kan jihohin da ƴan takarar suke da ƙarfi na samun ƙuri'u, waɗanda zasu lashe babu tantama.

Atiku Abubakar

Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ɗan jihar Adamawa ne a yankin Arewa maso gabas na Najeriya. Atiku ya nemi takarar shugabancin ƙasar nan har sau biyu amma bai taɓa nasara ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A shekarar 2019, shine ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa wanda shugaba Buhari ya lashe.

Hasashe ya nuna cewa ɗan takarar zai iya lashe jihohin Adamawa, Delta, Bayelsa, Akwa Ibom, Edo, Rivers da Cross Rivers da tazara mai yawa.

Dalili kuwa shine, jihar Adamawa mahaifar sa ce sannan kuma sauran jihohin da aka lissafo duk suna ƙarƙashin ikon jam'iyyar PDP ne.

Bola Tinubu

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shine ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa. Tinubu gogaggen ɗan siyasa wanda ya taɓa riƙe muƙaman sanata da gwamna har sau biyu a jihar Legas.

Kara karanta wannan

An Tafka Magudi: Dan Takarar Gwamnan PDP Yaki Yarda Da Kaddara, Zai Kalubalanci Sakamakon Zabe a Kotu

Wannan ne karon farko da Tinubu yake jaraba sa'ar sa wajen neman shugabancin Najeriya.

Hasashe ya nuna cewa Tinubu zai lashe kuri'un jihohin Kudu maso yammacin Najeriya.

Jihohin sun hada da Legas, Oyo, Ogun, Ogun, Ondo da Ekiti.

Babban dalili kuwa shine Tinubu dan yankin ne kuma kabilar Yarabawa ne. Sannan mafiya yawan jihohin yankin suna ƙarƙashin ikon jam'iyyar sa ta APC ne.

Rabiu Musa Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano ne kuma tsohon sanata wanda shine jagoran ɗarikar Kwankwasiyya.

Kwankwaso yana takarar shugaban ƙasa ne a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, wacce ya kafa ta musamman domin yayi takara a wannan zaɓen.

Hasashe ya nuna cewa ɗan takarar zai lashe wasu daga cikin jihohin yankin Arewa maso Yamma da wasu jihohin yankin Arewa maso Gabas.

Jihohin da ake sa ran Kwankwaso zai iya lashe wa sun hada da Kano, Katsina, Jigawa, Zamfara, Gombe, da Bauchi.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: An Taso Shugaban INEC Na Kasa a Gaba, Ana Neman Tilas Sai Yayi Abu 1 Rak

Babban dalili kuwa shine ɗan takarar ya fito ne daga yankin Arewa maso Yamma, sannan yana da ɗumbin magoya baya a sauran jihohin da aka lissafo. Rahoton Channels tv

Peter Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ne kuma gogaggen ɗan kasuwa.

Peter Obi yayi takarar mataimakin shugaban ƙasa a shekarar 2019 tare da Atiku Abubakar. Wannan ne karon farko da yake neman shugabancin Najeriya.

Hasashe ya nuna cewa Peter zai lashe jihohin yankin Kudu maso Gabas da jihar Benue. Rahoton Daily Trust

Jihohin sun haɗa da Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo.

Babban dalilin da ya sanya aka yi hasashen zai lashe waɗannan jihohin shine, ya fito ne daga yankin sannan kuma mutanen yankin sun daɗe suna son ganin sun shugabanci Najeriya.

A wani labarin kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta saki adadin yawan waɗanda suka karɓi katin zaɓe a Najeriya.

Hukumar ta kuma yi bayani dalla-dalla kan yawan masu kaɗa ƙuri'a na kowane yanki a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel