Matsin tattalin arziki
Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ce sun lura ‘yan siyasa su na sayen sababbi. Ana zargin Gwamnonin jihohi 10 ne suke sayen kudin, suna boyewa.
A yau ne aka zauna a kotu don duba yiwuwar tsawiata wa'adin daina amfani da tsoffin Naira. Kotun koli ta yi hukunci, ta bayyana lokacin da za a ci gaba da zama.
Za a ji matsayar duka 'yan takaran shugaban kasa a zaben 2023 bayan Bankin CBN da goyon bayan gwamnatin tarayya ya fito da sababbin N200, N500 da kuma N1000.
Mustapha Audu wanda shi ne Kakakin kwamitin yakin neman zaben APC a Arewa maso tsakiya, ya soki tsare-tsaren Gwamnatin Muhammadu Buhari na tattalin arziki.
Za a ji labari cewa canza kudi ya jawo Sarkin Iwo ya zama daidai da Maroki. Abdurosheed Akanbi ya ce ba zai iya bugun kirji ya ce yana da N20, 000 a yanzu ba.
'Yan POS da ke karbar sama da N200 wajen cire kudi za su fara fuskantar fushin doka nan ba da jimawa ba. CBN ya ce zai fara kama su a hankali nan kusa kadan.
A yau Talata, gwamnan babbam bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa babu bukatar sake tsawaita wa'adin karban tsoffin takardun naira a Najeriya.
Abin da Godwin Emefiele ya fada wajen taron majalisar magabata a yau ya bayyana. Gwamnan babban bankin ya ce a yanzu fa babu takardun da za a buga sabon kudi.
Makonni biyu da suka wuce aka ba wani banki sababbin kudi, har yau ba su fito da kudin ba. CBN yana zargin sauran bankuna da kawo tasgaro ta hanyar boye Nairori
Matsin tattalin arziki
Samu kari