Buhari Bai Yi Kokari Sosai a Nan ba, Jigon APC Ya Fadi Bangare 1 da Tinubu Zai Gyara

Buhari Bai Yi Kokari Sosai a Nan ba, Jigon APC Ya Fadi Bangare 1 da Tinubu Zai Gyara

  • Mustapha Audu yana ganin Muhammadu Buhari ya yi kura-kurai ta fannin tattalin arziki
  • Duk da haka, ‘Dan siyasar ya ce akwai bangarori da-dama da za a yabawa gwamnatin APC
  • Muddin Bola Tinubu ya lashe zabe, Audu ya ce gwamnatinsa za ta kawo manufofi na kwarai

Abuja - Kakakin kwamitin yakin neman zaben APC na shiyyar Arewa maso tsakiya, Mustapha Audu ya soki wasu tsare-tsaren Gwamnati mai-ci.

Da aka zanta da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Talata, Mustapha Audu ya nuna Muhammadu Buhari bai yi kokari sosai ta fuskar tattalin arziki ba.

Hakan yana zuwa a lokacin da ake jin wasu daga cikin shugabanni a jam’iyyar APC da masu mulki su na sukar tsarin canza manyan takardun kudi.

Lamarin ya kai wasu su na zargin an yi canjin ne da nufin jawowa ‘dan takarar APC bakin jini.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

APC ta fadawa masu mulki gaskiya

Audu ya shaidawa gidan talabijin jam’iyyar APC ta fito karara ta fadawa shugaban Najeriyan gaskiya ne, ta ki yabawa tsarin da ya gagara yin aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan siyasar ya ce Gwamnatin Muhammadu Buhari ta gyara wasu bangarorin, amma ya ce idan har aka zo batun tattalin arziki, akwai ta-cewa a nan.

Buhari
Shugaba Buhari da Tinubu a Imo Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

The Cable ta rahoto Audu yana mai cewa wasu manufofi da tsare-tsaren tattalin arzikin da shugaba Buhari ya fito da su, ba su haifi ‘da mai ido ba.

A cewarsa, idan Bola Tinubu ya yi nasara wajen darewa karagar mulki, zai gyara wadannan matsaloli da aka samu domin ya sa kan dawar garin.

“APC jam’iyya ce ta mutane dabam-dabam masu basra. Idan abubuwa na tafiya daidai, za a goyi bayansa; idan bai tafiya daidai, za a koka game da shi.

Kara karanta wannan

Sarkin Ibo Ya Yi wa Shugaban Kasa Abin da ba Zai Manta ba Har ya Bar Duniya

Babu bukatar a rika jinjinawa tsarin da bai aiki, dole ne a fadawa masu mulki gaskiyar lamari.
Mun zo ne a matsayin jam’iyya domin mu yaki wasu abubuwa tun farko. Shugaban kasa ya yi kokarin yakar rashin tsaro, da wasu abubuwa da-dama.
Mun fita daga matsin lambar tattalin arziki, shugaban kasa ya yi kokari kan COVID-19, yanzu yakin Ukraine da Rasha yana da tasiri a kan Najeriya.

- Mustapha Audu

Kiran Sarkin Iwo a kan canjin kudi

An ji labari Mai martaba Sarkin Iwo, Abdurosheed Akanbi ya na fatan Gwamnatin tarayya za tayi amfani da ranar masoya domin jin kan al’ummarta.

Sarkin yake cewa ‘Yan Najeriya su na shan wahala sosai, ya ce a matsayinsa na Basarake, ba zai iya bugun kirji cewa ya na da N20, 000 a fadarsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel