Ina Sane da Halin Kuncin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki, Buhari Ya Yi Magana Mai Daukar Hankali

Ina Sane da Halin Kuncin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki, Buhari Ya Yi Magana Mai Daukar Hankali

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba 'yan Najeriya bisa halin da suke ciki a wannan lokaci da suke yiwa kallon mai tsanani
  • Shugaban ya bayyana cewa, yana sane da duk wani hali da 'yan kasar ke ciki, kuma zai dauki matakin da ya dace
  • Saura kwanaki kadan a yi zaben shugaban kasa a Najeriya, Buhari ya bayyana dan takarar da ya kamata 'yan Najeriya su zaba

Najeriya - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya godewa 'yan Najeriya bisa zabensa da suka yi ya yi mulki a kasar har sau biyu; daga 2015 zuwa 2023.

Shugaban ya bayyana cewa, ya yaba da kokarin 'yan kasar bisa wannan karimci da suka ba shi na damar shugabantarsu.

Idan baku manta ba, saura kwanaki shida kacal a yi zabe a Najeriya, kuma shugaban kasa Buhari na da dan takarar da jam'iyyarsa ta tsayar don maye gurbinsa.

Kara karanta wannan

Hannunka mai sanda: Saura kwana 6 zabe, Buhari ya fadi dan takarar da ya kamata a zaba

Buhari ya tasauyawa 'yan Najeriya, ya ce su yi hakuri
Ina Sane da Halin Kuncin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki, Buhari Ya Yi Magana Mai Daukar Hankali | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Da yake yiwa 'yan Najeriya bayanan godiya a shafinsa na Facebook, Buhari ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"'Yan uwana 'yan Najeriya, ina so na yi amfani da wannan damar har ila yau don gode muku bisa zaba ta da kuka yi na zama shugaban kasa har sau biyu."

Ina sane da halin kuncin da kuke ciki, cewar Buhari

A bangare guda, shugaban kasan ya ba 'yan Najeriya hakuri bisa halin da ake ciki bisa sabbin ka'idojin da gwamnatinsa ta samar.

A cewarsa:

"Daga karshe, ina so na tabbatar muku cewa ina sane daram da halin kuci da kuke fuskanta saboda wasu ka'idojin da gwamnati ta kawo wadanda aka yi su da nufin kawo ci gaba ga kasar.
"Ina rokonku da kara hakuri yayin da muke daukar matakan da suka dace don saukake wadannan wahalhalu. Idan Allah ya yarda, akwai harke a nan gaba kadan."

Kara karanta wannan

Naira: Shugaba Buhari Na Yiwa Kotun Koli Karan-Tsaye, Bai Dace Ba: Kakakin Majalisa

Tinubu ne ya kamata ku zaba a zaben bana

A bangare guda, shugaban kasan ya bayyana cewa, akwai bukatar 'yan Najeriya su zabi Bola Ahmad Tinubu a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Buhari ya bayyana cewa, ya yarda da Tinubu, kuma tabbas shine zai yi abin da ya dace bayan ya sauka daga mulki.

Ya kuma bayyana cewa, shi ba dan takara bane, amma APC ta zabi Tinubu, kuma shi ma shine zabeninsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel