Babu Takardun Buga Sababbin Kudi – Gwamnan CBN Ya Fadi Gaskiyar Halin da Ake Ciki

Babu Takardun Buga Sababbin Kudi – Gwamnan CBN Ya Fadi Gaskiyar Halin da Ake Ciki

  • Godwin Emefiele ya sanar da majalisar magabata cewa babu takardun da za a buga sabon kudi
  • CBN ya yi canjin kudi a Najeriya, ana tsakiyar tsarin ne sai takardu suka karewa kamfanin NSPM
  • Gwamnan babban Bankin ya zargi bankuna da boye ‘yan sababbin kudin da aka iya bugawa a kasar

Abuja - A halin yanzu, ana fama da karancin takardun da za a buga takardun kudi. Gwamnan babban banki na CBN, Godwin Emefiele ya fadi haka.

A wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, an ji Godwin Emefiele ya koka a kan yadda karancin takardu ya kawowa tsarin da ya kawo illa.

CBN da Gwamnatin Muhammadu Buhari sun fito da tsarin takaita yawon kudi a al’umma, wanda hakan ya kawo zanga-zanga a wasu garurwa.

Da aka je taron majalisar magabata a fadar shugaban kasa, gwamnan babban bankin ya shaidawa mahalarta kamfanin buga kudi ya gamu da cikas.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari na ganawar sirri da gwamnan CBN bayan hukuncin kotun koli kan batun kudi

Da alama ba za a buga sababbin kudi ba

Matsalar da kamfanin NSPM ta samu ta jawo an gagara buga sababbin kudin da za su maye guraben tsofaffin N200, N500 da 'yan N1000 da aka karbe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Takardun kamfanin buga kudi sun kare balle a buga ‘Yan N500 da N1000.
Kamfanin ya na jiran isowar takardu daga wani kamfanin Jamus da kuma De La Rue, amma an zaunar da su tun tuni, ba za a iya amsa bukatarsu yanzu ba.

- Godwin Emefiele

Aso Rock
Taron Majalisar magabata Hoto: BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Babu halin buga N70m - Majiya

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa bankin na CBN ya umarci NSPM ya buga Naira miliyan 70 na sababbin kudi, kenan an iya buga Naira biliyan 126.

Abin takaicin shi ne kamfanin kasar ya sanar da babban banki cewa ba zai iya buga wadannan kudi a halin da ake ciki ba, alhali ana kukan karancin Naira.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan CBN ya warware zare da abawa ga shugaban INEC kan sabbin Naira

Duk da matsalar da ake samu daga bangaren hukuma, Godwin Emefiele ya yi taron bayanin yadda wasu ma’aikatan banki suke hana ruwa gudu a Najeriya.

A yayin da lokacin sallar juma’a ya gabato, Muhammadu Buhari ya tafi masallaci, sai ya bar Farfesa Yemi Osinbajo ya cigaba da jagorantar zaman majalisar.

Tsarin yana taba Tinubu?

A baya kun ji labari cewa wani matashin ‘dan PDP, Adnan Mukhtar T/Wada wanda ya shaida mana farin jinin Atiku Abubakar ya karu sosai yanzu a Kano.

Hadimin na Shugaban masu yakin takarar Atiku Abubakar, Ibrahim Little ya ce tsarin canza kudi ya jawowa jam'iyyar APC bakin jini sosai gabanin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel