Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

  • Mutanen Najeriya sun samu kan su a wani yanayi a dalilin canza wasu takardun kudi da aka yi
  • Bankin CBN da goyon bayan gwamnatin tarayya ya fito da sababbin N200, N500 da kuma N1000
  • Hakan ya raba kan Gwamnatin tarayya da wasu Jihohi, ‘yan takara sun tofa albarkacin bakinsu

Abuja - Canjin kudin da aka yi ya bar kasa a cikin mawuyacin hali. Hakan ya jawo Gwamnonin Jihohi suka bukaci ganawa da Muhammadu Buhari.

Bayan zaman Gwamnonin Najeriya da shugaban kasa, an kira taron majalisar magabata domin a bada shawarar yadda za a bullowa lamarin canjin.

An tattaro ra’ayin manyan masu neman takarar shugaban kasa a game da sabon tsarin tattalin arziki da aka fito da shi.

1. Bola Tinubu

A wani jawabi da ya fitar, Bola Tinubu ya bada shawarari shida a kan yadda za a magance matsalar da aka shiga, Daga ciki shi ne ayi amfani da tsohon kudi.

Kara karanta wannan

Ka kawo karshen yunwa da fatara: Kungiyar Musulmai ta roki Tinubu alfarma idan ya karbi mulki

Tinubu yana so bankuna su daina karbar kudi daga cinikin da aka yi ta manhajar banki ko POS, sannan gwamnati ta tursasa bankuna su inganta fasaharsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Dan takaran ya kuma bukaci hadin-kan hukumomin gwamnati irinsu NPA da ma’aikatar yada labarai domin ganin yadda za a ci moriyar tsarin na CBN.

Tinubu
'Dan takaran APC Bola Tinubu a Imo Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

2. Atiku Abubakar

Atiku Abubakar ya soki tsarin kamar sauran ‘yan takara, amma kuma ya ba gwamnatin tarayya shawara cewa ka da a canza wa’adin 10 ga watan Fubrairu.

Akwai masu ganin tun farko an fito da tsarin ne domin a taimaki takarar Atiku wanda ake ganin shi ne babban abokin hamayyar jam’iyyar APC a zaben 2023.

3. Peter Obi

A duk abin da aka yi, an rasa inda ‘dan takaran jam’iyyar LP, Peter Obi ya sa gaba. Ana zargin tun farko bai da ilmin tattalin arzikin da ake tunani.

Kara karanta wannan

Kasar Ingila ta Kakaba Takunkumi a kan ‘Yan Siyasa 10 a Najeriya Saboda Kalamansu

Abin da ya fito daga bakin ‘dan takaran shi ne mutane su kara hakuri da wannan mataki da babban bankin kasar ya dauka na canza wasu takardu kudi da sababbi.

4. Rabiu Kwankwaso

Kamar sauran ‘yan takaran jam’iyyun adawa, Rabiu Kwankwaso ya soki wannan tsari da cewa tun farko kuskure aka yi, ya kuma nuna ba ayi shawara da mutane ba.

‘Dan takaran na NNPP ya bada misali da lokacin da ya fito da tsarin biyan kudi ta yanar gizo a Kano, ya ce kafin ayi haka sai da aka kafa kananan bankuna 36.

Kiran Sarkin Iwo a kan canjin kudi

An ji labari Mai martaba Sarkin Iwo, Abdurosheed Akanbi ya na fatan Gwamnatin tarayya za tayi amfani da ranar masoya domin tausaya al’ummarta.

Sarkin yake cewa ‘Yan Najeriya su na shan wahala sosai, ya ce a matsayinsa na Basarake, ba zai iya bugun kirji cewa ya na da N20, 000 a fadarsa ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Asali: Legit.ng

Online view pixel