Jihar Bauchi
A maimakon tsohon Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed A. Abubakar ya bi bayan AVM Sidique Abubakar mai ritaya, yana tare da Gwamna Bala Mohammed ne a zaben 2023.
Bala Muhammed, gwamnan jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya ya nada mace ta farko da ta zama Farfesa a Bauchi LG a matsayin sabuwar VC a jami'ar jiha
Yan sanda a jihar Bauchi sun kama wani Haruna Ezekiel kan zarginsa da aikata kisar gillar kan kawunsa mai shekaru 80 da ya zarga da maita bayan ya ba dansa nama
Shugaba Muhammadu Buhari ya bi sahun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wajen aike sakon gaisuwa ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda bai da lafiya
Rukaiya Atiku Abubakar, matar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ta bugi kirji ta ce mijinta ne ya ke da tsari mafi kyau ga mata da matasan Najeriya.
Gabannin babban zaben 2023, jam'iyyar APC ta yi babban rashi na wani jigonta, Alhaji Mahmoud Maijama’a, wanda ya nemi takarar gwamna a Bauchi. Ya koma PDP.
Yan sanda sun kama wani Michael Joseph, dan damfarar ATM a jihar Bauchi dauke da katin ATM daban-daban guda 31 yayin da ya yi kokarin damfara wata baiwar Allah.
Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Usman Tilde, yayi murabus. Kwashi nan ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook inda ya bayyana dalilin hakan.
Za a ji fada ya kaure tsakanin mutanen Gombe da Bauchi kan mallakar rijiyoyin man Kolmani. Mutanen Gombe sun zargi Muhammadu Buhari da kokarin karbe dukiyarsu.
Jihar Bauchi
Samu kari