Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Babban Dan Kasuwa a Bauchi

Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Babban Dan Kasuwa a Bauchi

  • ‘Yan bindiga sun hallaka wani matashin dan kasuwa a kauyen Balele da ke karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi
  • Mazauna kauyen sun tabbatar da haka inda suka ce an kashe Chinonso Ugwu a kauyen da misalin karfe 1:30 na dare
  • Mataimakin shugaban karamar hukumar na rikon kwarya, Muhammad Lawan ya tabbatar da faruwar lamarin ga ‘yan jaridu

Jihar Bauchi – Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun hallaka wani dan kasuwa a kauyen Balele da ke karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Marigayin mai suna Chinonso Ugwu an kashe shi ne da misalin karfe 1:30 na dare a ranar Talata 11 ga watan Yuli.

Masu Garkuwa Ne Sun Hallaka Wani Matashin Dan Kasuwa A Bauchi
Masu Garkuwa Sun Addabi Kauyuka Da Dama Musamman Karamar Hukumar Ningi Ta Jihar Bauchi. Hoto: The Guardian.
Asali: UGC

Wani mazaunin kauyen da yaki bayyana sunansa ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun durfafi kauyen ne a ranar Talata da tsakar dare inda suka yi ta harbi sama, Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yadda Tarin Shara Ya Hana Masu Abin Hawa Bin Babban Titi a Birnin Kano, ‘Yan Kasuwa Sun Koka

Yadda 'yan bindigan suka hallaka matashin

Ya ce ‘yan bindigan sun bindige wani dan kasuwa mai shekaru 37 a duniya inda suka yi ta harbinshi a ciki da kuma kai, cewar Daily Post.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa babu wanda ya zo wurin don cetonshi saboda tsoron kada shi ma ya shiga tarkonsu, har sai washe gari ne aka dauke shi zuwa asibiti tare da rakiyar ‘yan sanda.

Ya ce:

“Har ila yau, wani likita ya bayyana rasuwarshi lokacin da suka isa babban asibitin Burra.”

Mataimakin shugaban karamar hukumar Ningi na rikon kwarya, Lawan Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch.

Ya ce bayan ya samu labarin harin ne ya tara jami’an tsaron soja da ‘yan sanda don ceto wanda abin ya shafa da kuma kare lafiyar mutane.

Kara karanta wannan

Radadin Cire Tallafi: Martanin 'Yan Najeriya Kan Aniyar Tinubu Na Raba N8000 Ga Gidaje 12m

Mataimakin shugaban karamar hukumar ya yi martani game da harin

A cewarsa:

“’Yan bindigan sun kwankwasa masa kofa lokuta da dama amma ya ki budewa, ya tsare bakin kofar ta ciki don hana su shiga.
“A lokacin ne suka harbi kofar sau da yawa, inda shi kuma harsashin ya ya same shi ya fadi.”

Kokarin samun martini daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ci tura sakamakon rashin samun shi da aka yi ta kiran waya.

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Tasa Keyar Mutum Hudu a Jihar Bauchi

A wani labarin, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tasa keyar wasu mutane hudu.

Yayin sace mutanen hudu 'yan bindigan sun raunata wani mutum daya a karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

'Yan bindigan sun durfafi kauyen Gamji inda suka yi awun gaba da wani mai suna Daniel.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel