Jihar Bauchi Ta Yi Babban Rashi, Farfesa Abdu Ibrahim Ya Kwanta Dama

Jihar Bauchi Ta Yi Babban Rashi, Farfesa Abdu Ibrahim Ya Kwanta Dama

  • Abdu Ibrahim, farfesa na farko a bangaren tiyatar kwakwalwa a jihar Bauchi ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya
  • Farfesa Ibrahim ya rasu ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, a asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) Bauchi
  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi alhinin mutuwar marigayin a cikin wata sanarwa da daya daga cikin hadimansa ya saki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Bauchi - Allah ya yi wa fitaccen likitan nan na kwakwalwa, Farfesa Abdu Ibrahim, rasuwa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Farfesa Ibrahim ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke jihar Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi
Jihar Bauchi Ta Yi Babban Rashi, Farfesa Abdu Ibrahim Ya Kwanta Dama Hoto: Babugirma Bauchi
Asali: Facebook

Gwamna Mohammed ya yi alhinin mutuwar Abdu Ibrahim, farfesan tiyatar jijiya na farko a Bauchi

Gwamna Mohammed ya yi alhinin mutuwar Abdu Ibrahim, farn Yuni, bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

A Ci Gaba Da Gashi: Gwamnan Arewa Ya Kara Hutun Sallah Har Zuwa Ranar Juma'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya shahara sosai kasancewar shine farfesan bangaren tiyatar kwakwalwa na farko a jihar Bauchi.

Da yake martani ga mutuwarsa, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana mutuwar Farfesa Ibrahim a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kadai ba har ma ga al’umar jihar Bauchi da ma kasa baki daya, rahoton Leadership Hausa.

Bayanan gwamnan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mukhtar Gidado, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin labarai ya saki a ranar Juma'a, 30 ga watan Yuni.

Sanarwar ta ce:

"Gwamna Bala Mohammed, a madadin iyalinsa, gwamnatin jihar Bauchi da mutanen kirki na jihar Bauchi, ya mika ta'aziyyarsa ga ahlinsa, abokai, abokan aiki, hadimai da mutanen jihar Bauchi gaba daya.
"Ya roki Allah ya saka masa da Aljannar Firdausi sannan ya baiwa danginsa da mutanen jihar Bauchi hakurin jure wannan rashi."

Kara karanta wannan

An Zargi Tsohon Ministan Buhari Da Yin Barazana Ga Rayuwar Na Hannun Daman Atiku

Jama'a sun yi martani a kan mutuwarsa

@realniceking ya rubuta a Twitter:

"Allah ya sa ya huta a jannatul firdaus"

@usman38005860 ya ce:

"Allah jiqansa da rahama."

@shasiibrahim ya rubuta:

"Allah ya gafarta masa kura-kuransa sannan ya sa Aljannat Firdause ta zama makomarsa...amin."

Tsohon Ministan Tsaro, Janar Bashir Magashi Bai Mutu Ba

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wani binciken kwakwaf da aka gudanar ya nuna rahoton da ke yawo na cewar tsohon ministan tsaro, Janar Bashir Magashi ya mutu ba gaskiya bane.

Wani wallafa da aka yada a dandalin WhatsApp ya yi ikirarin cewa tsohon ministan tsaron, ya mutu a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni. R

Asali: Legit.ng

Online view pixel