Arewa
Jami'an tsaron haɗin guiwa sun samu nasara aika yan bindiga 67 barzahu kana suka ceto fiye da murum 20 da aka yi garkuwa da su a jihar Bauchi da ke Arewa.
Yan sanda sun yi nasarar kame wasu tsagerun 'yan bindigan da ake zargin sun sace wasu mutane tare da hallaka wasu dama a yankin Zaria da ke Kaduna.
Majalisar jihar Kano ta karrama Auwalu Salisu da lambar yabo da kuma kudade har Naira miliyan 1.5 kan abin da ya aikata na mayar da miliyan 15 da aka bari a kekensa.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya amince da biyan makudan kudaden makaranta ga dalibai 'yan asalin jihar da ke sauran Jami'o'in Najeriya don kammala karatunsu.
An bayyana yadda sojojin Najeriya suka yi nasarar hallaka 'yan ta'adda a yankuna daban-daban an Arewacin Najeriya da kuma kame wasu da dama a mako 1.
Dan majalisa a jihar Kano mai wakiltar mazabar Tarauni a majalisar Tarayya, Mukhtar Yerima ya yi nasarar kwato kujerarsa a kotun daukaka kara bayan ya rasa kujerarsa
Kwamishinan yada labarai a jihar Benue, Matthew Abo ya shaki iskar 'yanci da safiyar yau Alhamis 5 ga watan Oktoba, an sace kwamishinan ne a gidansa da ke Zaki-Biam.
Jami'an 'yan sanda sun kwamushe wani da ake zargin ya na bai wa 'yan bindiga bayanan sirri da ya kai ga sace daliban Jami'ar FUDMA a jihar Katsina.
Rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa ta kama wani dan Jamhuriyar Nijar, Bilal Faraji da wasu mutane biyar kan zargin safarar muggan makamai da kuma sata.
Arewa
Samu kari