Dama Dino Melaye Bai Cancanci Zama Gwamna Ba, Wike Ya Tono Asirin Dan Takarar Gwamnan PDP a Kogi

Dama Dino Melaye Bai Cancanci Zama Gwamna Ba, Wike Ya Tono Asirin Dan Takarar Gwamnan PDP a Kogi

  • Siyasar PDP na ci gaba da damewa tun bayan da aka kammala zaben shugaban kasa na wannan shekarar da ake ciki
  • Wike ya ce Dino Melaye bai cancanci zama gwamnan jihar Kogi ba, don haka PDP ta yi kuskure a zaben dan takararta
  • An yi zabe a Kogi, an bayyana wanda ya lashe zaben da aka dade ana jiran faruwarsa kuma ya faru a karshen mako

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT) kuma tsohon gwamnan jihar Ribas ya caccaki tikitin takarar gwamna da aka baiwa Sanata Dino Melaye a karkashin PDP.

Wike, a cikin wani tsohon faifan bidiyo da ke ci gaba da yawo ya bayyana cewa tun farko jam’iyyar PDP a jihar Kogi ta baiwa Dino Melaye tikitin takarar gwamna ba karamin kuskure bane.

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: a karshe, Dino Melaye ya yi martani kan dokuwa da yake a zabe, ya fadi abin da INEC za ta yi

Melaye bai cancanci zama gwamna ba, inji Wike
Wike ya caccaki Dino Melaye | Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Senator Dino Melaye
Asali: Facebook

Wike ya bayyana cewa, PDP bata dauko hanyar nasara ba tunda ta ba Melaye damar yin takarar gwamna a jihar ta Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Melaye bai cancanci zama gwamna ba, inji Wike

A cewar Wike, Melaye ba shi da abin da ake bukata don zama gwamna, saboda a cewarsa, Melaye ba mutum ne da ya cancanta ba.

Ministan babban birnin tarayya ya lura cewa Melaye ya san yadda ake hayaniya a gidan talabijin na kasa amma bai fahimci yadda ake tafiyar da harkokin mulki ba.

Bidiyon Wike ya fito ne bayan dan takarar jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kogi, Usman Ododo ya doke Melaye a rumfar zabensa inda ya lashe kananan hukumomi 11 cikin 18 da INEC ta sanar.

Yadda bidiyon ke yawo

Bidiyon da wani mai amfani da manhajar X mai suna @DeeOneAyekooto ya yada a ranar Lahadi, Nuwamba 12, a halin yanzu yana ci gaba a jan hankali a dandalin sada zumunta.

Kara karanta wannan

INEC ta dage tattara sakamakon zaben gwamnan Bayelsa, cikakken bayani ya bayyana

Wike ya ce:

"Ba maganar nahawu muke ba, maganar gwamnan wata jiha muke yi, saboda Allah, PDP ta gabatar da irin wannan dan takara kuma kuna nufin mutanen Kogi suna son ci gaba?"

Ba sabon abu bane Wike ya soki 'yan PDP duk da dan cikinta ne tun bayan da ya fara rabar jam'iyyar APC da fara cin moriyarta.

Kalli bidiyon:

Ododo ya lashe zaben Kogi

A wani labarin, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Usman Ododo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, rahoton Tribune Online.

Baturen zabe Johnson Urama na Jami’ar Najeriya da ke Nssuka ne ya sanar da sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Lokoja, babban birnin jihar a daren Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.