Shehu Sani Ya Tona wa Yan Siyasa Asiri, Bai Cire har Yan Jam’iyyar APC Ba

Shehu Sani Ya Tona wa Yan Siyasa Asiri, Bai Cire har Yan Jam’iyyar APC Ba

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce manyan 'yan siyasar Najeriya na jam'iyyar mulki da 'yan adawa duk ɗaya suke
  • Ya bayyana cewa da dama daga cikin 'yan siyasar da ke adawa da juna a yanzu sun taɓa kasancewa abokan siyasa kuma sun yi aiki tare
  • Shehu Sani ya ce zaɓin da ke gaban 'yan Najeriya ya taƙaita ne tsakanin ƙungiyoyin manyan masu jari-hujja da ke mulki da waɗanda ke adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan bambancin akida tsakanin jam'iyyar da ke mulki da 'yan adawa a Najeriya.

Shehu Sani ya ce da dama daga cikin 'yan siyasar da ke ɓangarorin adawa da na gwamnati a yanzu sun taɓa kasancewa abokan siyasa, suna aiki tare tare da kare muradunsu.

Shehu Sani ya tona wa yan siyasa asiri
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani. Hoto: Shehu Sani.
Source: Facebook

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne yayin wani tsokaci kan siyasar Najeriya, inda ya ce tarihin alaƙar 'yan siyasar ya sa suka fahimci dabarun juna da yadda ake fafatawa a siyasa, cewar TVC News.

Ya fadi yadda 'yan siyasa ke kallon juna

A cewarsa, 'yan siyasar da suka taɓa kasancewa a ƙungiya ɗaya sun san yadda siyasar ke gudana, ciki har da abubuwan da suka dace da waɗanda ba su dace ba.

Ya ce talakawa kan ɗauki 'yan siyasar da suke goyon baya a matsayin mutanen kirki, yayin da suke ganin waɗanda ba sa tare da su a matsayin miyagu.

Shehu Sani ya ce:

“Idan kai ɗan kallo ne, kana kallonsu a matsayin waliyyai da masu zunubi, amma su a matsayinsu na 'yan wasan siyasa da suka taɓa buga wasa a ƙungiya ɗaya, sun san cewa babu waliyyai a cikin wannan wasa.”
Shehu Sani ya ba yan Najeriya shawara
Dan takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani. Hoto: Shehu Sani.
Source: Facebook

Shehu Sani ya yi wa yan siyasa kudin goro

Shehu Sani ya bayyana jam'iyyar APC mai mulkin kasar da 'yan adawa a matsayin yan jari-hujja.

Tsohon sanatan ya ƙara da cewa zaɓin da ke gaban 'yan Najeriya ya taƙaita ne tsakanin manyan masu jari-hujja da ke riƙe da madafun iko da waɗanda ke cikin ɓangaren adawa.

Ya ce:

“Zaɓin da ke gabanku shi ne tsakanin Ƙungiya A, wato manyan masu jari-hujja da ke kan mulki, da Ƙungiya B, wato manyan masu jari-hujja da ke ɓangaren adawa.”

Haka kuma, Shehu Sani ya bayyana cewa dukkan ɓangarorin biyu suna bin tsarin tattalin arzikin Bretton Woods, duk da bambancin jam'iyyun siyasar da suke wakilta.

Tsarin Bretton Woods ya samo asali ne bayan Yaƙin Duniya na Biyu, kuma ya shafi tsarin tattalin arziki da kuɗi na duniya, musamman ta hannun hukumomi irin su Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya.

Abin da ke jawo kashe malamai - Shehu Sani

An ba da rahoton cewa tsohon Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilai uku da yake ganin suka jawo kashe fitattun malaman addini a Arewa.

Shehu Sani ya ce malaman sun yi fice wajen yin Allah-wadai da tsattsauran ra’ayi, inganta zaman lafiya da kuma jure wa bambancin addinai.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa ‘yan ta’adda suna son a yi shiru, yana mai cewa duk wanda ya yi magana kan ta’addanci na iya fuskantar barazana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.