An Fadi Lokacin da Tinubu ke Bukata domin Seta Najeriya Ta Dawo Hayyacinta

An Fadi Lokacin da Tinubu ke Bukata domin Seta Najeriya Ta Dawo Hayyacinta

  • Tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Yakubu Danjuma, ya buƙaci ƴan Najeriya su sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Danjuma ya ce wa'adin mulki ɗaya ba zai isa Tinubu ya kammala ayyukan da gwamnatinsa ta fara ba
  • Tsohon hafsan sojin ya kuma bayyana cewa Tinubu ya naɗa Kiristoci da dama a mukaman gwamnati, yana mai cewa hakan ya nuna adalci da haƙurinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Yakubu Danjuma mai ritaya, ya ba ƴan Najeriya shawara kan sake zaben Bola Tinubu.

TY Danjuma ya bukaci su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 domin bai wa gwamnatinsa damar kammala ayyukan da ta fara.

TY Danjuma ya bukaci sake ba Tinubu dama
Janar TY Danjuma mai ritaya tare da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Janar Danjuma ya yi wannan kira ne a wajen bikin cika shekaru 20 da kafuwar ɗakin ibadar Kiristoci da ke gidan gwamnatin jihar Adamawa, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

An yi gamon katar: Abin da Tinubu ya fada wa Fubara bayan APC ta hana shi takara

Ya jaddada cewa wa'adin mulki na farko na Shugaba Tinubu ba zai wadatar wajen kammala shirye-shirye da ayyukan da gwamnatinsa ta fara ba.

Dalilin da ya sa Danjuma ke son a zaɓI Tinubu

Tsohon ministan, wanda tsohon shugaban hafsoshin sojin ƙasa, Janar Ishaya Bamaiyi, ya wakilta a wajen taron, ya ce Tinubu ya naɗa Kiristoci da dama a muƙaman gwamnati.

A cewarsa, wannan mataki ya nuna adalci da haƙurin shugaban ƙasar da ke neman wa'adi na biyu.

Danjuma ya buƙaci ƴan Najeriya, musamman mutanen yankin Middle Belt, da su mara wa Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a watan Janairun 2027.

Danjuma ya yi alkawarin bayar da miliyoyin kudi

A yayin taron, tsohon ministan ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 250 domin tallafa wa aikin faɗaɗa ɗakin ibadar Kiristocin da ke gidan gwamnatin Adamawa.

Ya bayyana cewa ana buƙatar ɗan Adam ya kasance yana da alaƙa da Mahaliccinsa, yana mai kira ga mabiya addini da su riƙa tsoron Allah a dukkan lamuransu domin samun shiriya da albarka.

Kara karanta wannan

Akpabio ya fadi miliyoyin kuri'un da zai samawa Tinubu a 2027

Oluremi ta shawarci matasa
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu. Hoto: Senator Oluremi Tinubu.
Source: Facebook

Remi Tinubu ta gargaɗi matasa kan siyasa

A nata jawabin, uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta gargaɗi matasa da kada su bari ƴan siyasa masu matsananciyar neman mulki su yi amfani da su wajen tayar da tarzoma.

Oluremi, wadda mataimakiyar gwamnan Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta, ta wakilta, ta buƙaci matasa su zama jakadun zaman lafiya da sauyi mai kyau.

Ta jaddada muhimmancin ɗabi'a mai kyau kafin zaɓen 2027, lokacin zaɓen da kuma bayan kammala zaɓen, cewar Punch.

An fadi barzanar da Tinubu ke fuskanta

Mun kawo maku rahoton cewa lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama, Deji Adeyanju, ya bayyana babbar barazanar da ke tunkarar.

Shugaba Tinubu kan tazarce Adeyanju ya danganta hasashensa da yanayin siyasa da ra'ayin al'ummar Arewacin Najeriya.

Kalaman nasa sun fito ne a daidai lokacin da kotu ta soke shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark da tsarin da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.