Kano: Mawaki Ya Maka BBC Hausa a Kotu Kan Dalili Daya Tak, Ya Nemi Diyyar Miliyan 120

Kano: Mawaki Ya Maka BBC Hausa a Kotu Kan Dalili Daya Tak, Ya Nemi Diyyar Miliyan 120

  • Mawakin Hausa a jihar Kano ya maka gidan jaridar BBC Hausa a kotu saboda satar fasaha
  • Mawakin mai suna Abdul Kamal ya maka BBC ne saboda yin amfani da wakarsa a wani shirinsu
  • Lauyan mai kara, Barista Ibrahim Umar ya roki kotun ta tilasta BBC biyan diyyar miliyan 120

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Mawakin Hausa a jihar Kano, Abdul Kamal yam aka gidan jaridar BBC Hausa a kotu kan zargin satar fasaha.

Mawakin ya maka BBC Hausa ne saboda su na amfani da wakarsa a cikin shirinsu na ‘Daga bakin mai ita’ ba tare da amincewarshi ba.

Mawakin jihar Kano ya maka BBC Hausa a kotu kan satar fasaha
Mawakin ya nemi diyyar miliyan 120. Hoto: Punch.ng.
Asali: UGC

Mene lauyan mai kara ke cewa?

Lauyan mawakin mai suna Barista Bashir Ibrahim ya fada wa kotu cewar yin amfani da wakar mawakin da BBC ta yi babu amincewarsa karya doka ne.

Kara karanta wannan

Ka Canza Hali: Tsohon Shugaba a APC Ya Fadi Kuskuren Tinubu Daga Shiga Aso Rock

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa hakan zai zubar wa matashin mawakin kimarsa tare da lalata masa sana’a a nan gaba, cewar Daily Trust.

Ya ce:

“A matsayinshi na matashin mawaki mai tasowa, wannan abin da BBC Hausa ta yi zai lalata masa sana’a.
“Mutane za su yi tunanin mawakin ya na amfani da sautin na BBC Hausa ne don neman suna.”

Martanin BBC Hausa kan shari'ar?

Lauyan ya kara da cewa su na bukatar BBC Hausa ta biya matashin naira miliyan 120 saboda barnar da su ka yi masa.

Baristan ya roki kotun da ta dakatar da BBC Hausa wurin ci gaba da amfani da sautin wakar mawakin har sai an kammala shari’ar.

A martaninshi, lauyan BBC Hausa, Barista Shakirudden Mosobalage ya fada wa kotu cewar BBC Hausa ta sayi sautin ne daga wani kamfani a Abuja.

Kara karanta wannan

"Ina yawan ganinsa a mafarki", matashin da ya kashe mahaifinsa a Kaduna ya fadi dalili

Ya bukaci kotun ta basu lokaci don gabatar da takardun da za su kare kansu a shari’ar da ake yi, cewar Aminiya.

Alkalin kotun, Mai Shari’a, N. M. Inusa ya dage ci gaba da sauraran karar har zuwa 12 ga watan Disamba.

Shehu Sani ya yi martani kan shari’ar Abba Kabir

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya roki kotun daukaka kara da ta bar Abba Kabir na jihar Kano a kujerarshi ta gwamna.

Har ila yau, sanatana ya kuma shawarci kotun da kada ta raba Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau da kujerarshi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel