Arewa
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta yi nasarar kwamushe wasu 'yan daudu guda 8 da ke tikar rawa a wurin bikin uban gidansu a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya umarci tantance karin mutane 147 don yi mu su auren gata a jihar kamar yadda aka yi a baya na aurar da mutum 1,800.
Hukumar NEMA ta bayyana cewa a halin yanzu an ceto mutane 12 da ransu yayin da wasu 17 suka mutu a haɗarin jirgin ruwan Taraba, an shiga kwana na uku.
Rundunar sojoji a jihar Kebbi ta yi ajalin wani kasurgumi kuma kwamandan 'yan bindiga, Mainasara da wasu biyu a jihar Kebbi a wani mummunan hari da ta kai.
Mambobin ƙungiyar ma'aikatan majalisar dokoki ta Najeriya reshen jihar Kano sun rufe zauren majalisa yayin da suka fara yajin aikin sai baba ta gani ranar Litinin.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya ankarar da cewa idan ba a yi da gaske ba dangane da Boko Haram, zata iya shafe Najeriya daga taswira.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya dauki nauyin jinyar yarinya Asmau Sani da ke fama da ciwon daji a asibitin Dala inda a ba da miliyan 1.5.
Wani abin bakin ciki ya faru a jihar Taraba yayin da jirgin ruwa dauke da fasinjoji fiye da 100 ya kife a tsakiyar rafi a ranar Asabar. An gano wasu gawarwaki.
Wasu fusatattun matasa sun yi wa wani Fasto tsinannen dukan kawo wuka tare da hadiminsa a coci a jihar Benue kan zargin sace mazakutar wani matashi.
Arewa
Samu kari