Budurwa Ta Riga Mu Gidan Gaskiya Suna Tsaka Da 'Holewa' Da Saurayinta Mai Sana'ar Aski a Kwara

Budurwa Ta Riga Mu Gidan Gaskiya Suna Tsaka Da 'Holewa' Da Saurayinta Mai Sana'ar Aski a Kwara

  • Rundunar ‘yan sanda ta kama wani matashi a unguwar Temidire da ke birnin Ilorin a jihar Kwara kan zargin ajalin budurwa
  • Matashin mai suna Isaac ana zargin ya sha maganin karfin maza don burge budurwarshi inda daga bisani ta rasa ranta
  • Kakakin rundunar a jihar, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Talata 31 ga watan Oktoba inda ya ce sun fara bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara – Wata budurwa ta gamu da ajalinta yayin da su ke tsaka da saduwa da saurayinta bayan ya sha maganin karfin maza.

Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin a jiya Talata 31 ga watan Oktoba a wani otal da ke unguwar Temidire da ke Ilorin a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta shiga tsakani a rigimar Gwamna Fubara da majalisar dokokin jihar Ribas

Saurayi ya yi ajalin budurwarsa bayan ya sha maganin karfin maza a Kwara
'Yan sanda sun cafke saurayin da ya yi ajalin budurwarsa da maganin karfin maza. Hoto: Kwara Police Command.
Asali: Facebook

Mene ake zargin saurayin a Kwara?

Saurayin mai suna Isaac mai sana’ar aski ya dauki matakin shan maganin ne don burge budurwar ta shi, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta ce yayin da su ke tsaka da saduwar, budurwar ta yi korafin cewa ta gaji amma saurayin bai ko juyo ta kanta ba.

Cewar majiyar:

“Yayin da su ke saduwar, budurwar ta fada ma sa cewa ta na jin zafi kuma ta gaji amma bai kulata ba inda daga bisani jini ya fara fita daga jikinta.
“A wannan lokaci ne ta shiga wani yanayi inda aka garzaya da ita asibiti wanda a can ta ce ga garinku.”

Wane martani ‘yan sanda su ka yi Kwara?

Daily Trust ta tattaro cewa saurayin ya nemi agajin ma’aikatan otal din bayan faruwar lamarin inda su ka kawo dauki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ajalin babban mai sarautar gargajiya, sun sace matarsa, dansa da wasu mutum 8

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun cafke saurayin kuma su na kan bincike.

Ya ce:

“Jami’anmu sun kama saurayin kuma mu na kan bincike don sanin ainihin abin da ya faru tsakaninsu a yayin saduwar.”

Bishiya ta yi ajalin wasu mutum 2 a jihar Kwara

A wani labarin, iftila’i ya afku a jihar Kwara bayan wata katuwar bishiya ta fado kan wasu mutane.

Lamarin ya jawo rasa rayukan mutane guda biyu yayin da dama su ka samu raunuka dalilin haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel