Satar Mazakuta: Matasa Sun Yi Wa Malamin Addini Dukan Kawo Wuka Kan Yashe Mazakutar Wani

Satar Mazakuta: Matasa Sun Yi Wa Malamin Addini Dukan Kawo Wuka Kan Yashe Mazakutar Wani

  • Wasu fusatattun matasa sun jikkata wani Fasto da hadiminsa kan zargin satar mazakutar wani matashi a Makurdi da ke jihar Benue
  • Ana zargin Faston da hadiminsa da satar mazakuta bayan wani matashi ya sanar da jama’a cewa ya rasa mazakutarsa a lokacin
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta kwatanta shi da abin takaici

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue – Wani Fasto da hadiminsa a cocin New Generation sun tsallake rijiya ta baya bayan zargin batar mazakuta a jihar Benue.

Ana zargin Faston ne bayan wani matashi ya rasa mazakutarsa a unguwar New Layout da ke Kanshio a bayan garin Makurdi babban birnin jihar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban karamar hukuma a Benue bayan sace shi na kwanaki

Matasa sun yi wa Fasto dukan mutuwa kan zargin satar mazakuta a Benue
Jama'a na daukar doka a hannu kan zargin satar mazakuta. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Meye ya faru da Fasto kan zargin satar mazakuta?

Rahotanni sun tabbatar da cewa Faston da mai taimaka masa a cocin sun sha dukan kawo wuka a hannun wasu fusatattun matasa a karshen mako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani shaidan gani da ido ya ce wani matashi ne ya sanar da jama’a cewa ma’aikacin cocin ya sace masa mazakuta inda jama’a su ka masa dukan kawo wuka.

Ya ce:

“Mu na zargin sai da ya ga ya kusa mutuwa ne sai ya ke fadawa mutane cewa Faston ne ya umarce shi da ya sace mazakutar wani don kai masa.”

Meye ‘yan sanda su ka ce kan satar mazakuta?

Vanguard ta tattaro cewa wanda ake zargin ya jagoranci mutane zuwa gidan Faston inda shi ma jama’a su ka ma sa dukan mutuwa.

An tabbatar cewa lokaci kadan ya rage dukkan wadanda ake zargin su rasa rayukansu kafin zuwan jami’an ‘yan sanda da su ka ceci rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Basarke Da Mutum 5 a Zamfara

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce wannan abin Allah wadai ne da kuma takaici.

Matasa sun yi ajalin wani Alhaji kan zargin satar mazakuta

A wani labarin, wasu fusatattun matasa sun yi ajalin wani Alhaji Tijjani Yakubu a birnin Abuja kan zargin satar mazakuta.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin yawar satar mazakuta ta yi yawa a tsakanin al’ummar Najeriya.

A kwanakin baya, Sanata Shehu Sani ya gargadi jama’a kan daukar doka a hannu inda ya ce sharrin matsafa ce kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel