Arewa
Rundunar sojin Najeriya ta yi ajalin mayakan Boko Haram 6 a jihar Yobe yayin ta cafke wasu mutane biyu da ke safarar miyagun makamai a jihar Kaduna.
Jigon APC kuma tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar a Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya soki tsarin shugabancin jam'iyyar inda ya ce a hankali sun dawo PDP.
Wasu matasa sun yi ajalin wani mutum mai suna Alhaji Tijjani Yakubu kan zargin satar mazakuta a Abuja, likitoci sun tabbatar da mazakutar na nan.
Majalisar Dattawa a yau Laraba 25 ga watan Oktoba ta rantsar da Amos Yohanna na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya maye gurbin Sanata Elisha Abbo na jam'iyyar APC.
Kotun ta fara sauraran shaidu a shari'ar da ake yi na kisan gillar da aka yi wa Manjo-Janar Idris Alkali Mohammed a karamar hukumar Jos ta Kudu da ke jihar Plateau.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Adamu Fika ya riga mu gidan gaskiya a daren jiya Talata 24 ga watan Oktoba yayin da ya ke dawo wa daga Ingila.
Attajirin ɗan kasuwan nan ɗan asalin jihar Kano, Alhaji Aminu Ɗantata, ya ƙara yin babban rashi, ɗaya daga cikin jikokinsa, Batulu, ya riga mu gidan gaskiya.
An bayyana yadda wasu sojojin Najeriya suka samu nasarar hallaka wani kasurgimin dan bindigan da ya addabi wani yankin jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas.
Wasu mutane biyu sun mutu yayin da wasu guda 10 su ka jikkata bayan wata katuwar bishiya ta fado kansu a jihar Kwara yayin da su ke jiran motar kasuwa.
Arewa
Samu kari