Jihar Adamawa
Yayin da ake kawo karshen zaben gwamna a jihar Adamawa yau 15 ga watan Afrilu, 2023, mun haɗa maku abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da manyan yan takara 2.
Gabannin fara zaben cike gurbi da za a yi, a nan mun kawo maku yawan kuri’un da yan takarar gwamna na jam'iyyun APC da PDP ke da su a jihohin Adamawa da Kebbi.
A nan akwai jerin manyan yan takara da kallo ke kansu yayin da hukumar zabe ke shirin gudanar da cikon zabe jihohin Adamawa, Kebbi da sauransu a yau Asabar.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Adamawa, ta kammala rarraba kayan aikin zaɓen cike gurbin gwamnan jihar, na ranar Asabar 15 ga Afirilu.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Adamawa, ta bayyana shirin ta na yin nasara a zaɓen cike gurbin gwamnan jihar na ranar Asabar. Tace ta shirya tsaf
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya nemi masu kaɗa kuri'a su dangwalawa jam'iyyar PDP a cikon zaben jihohin Adamawa da Kebbi gobe Asabar.
Jam'iyyar PDP ta tubure inda ta bayyana cewa lallai sai dai a sauke Mallam Hudu Yunusa Ari daga matsayin kwamishinan zaben jihar Adamawa kafin ran 15 ga Afrilu.
'Yan sanda a jihar Adamawa sun tabbatar da an kashe mutane uku a wani farmakin da 'yan bindiga suka kai wani yankin karamar hukumar Hong da ke jihar ta Arewa.
Yayin da ake dambarwa kan kujerar shugaban PDP na kasa, babbar kotun tarayya mai zama a Yola ta kwace kujerar ɗan majalisar dokokin jihar Adamawa kan abu 1.
Jihar Adamawa
Samu kari