Jihar Adamawa
Bayan korarsa daga aiki da Bola Tinubu ya yi, tsohon kwamishinan INEC a jihar Adamawa, Hudu Ari, ya jaddada cewa Sanata Aisha Binani ce ta lashe zaben gwamna.
An yi rashin babban malamin Musulunci a jihar Adamawa, Sheikh Abubakar Daware, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya tura sakon ta'azziya.
Wasu bama-bamai da aka binne a hanyar Borno zuwa Adamawa ta yi sanadin mutuwar mutum 2, bayan motarsu da ke kan hanyar kasuwa ta taka IED a hanyar zuwa kasuwa.
Dan uwan Malam Nuhu Ribadu ya zama sarki bayan Gwamna Ahmadu Fintiri ya nada shi a matsayin Sarkin Fufore, sabon masarautar da aka kafa a jihar Adamawa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohuwar ƴar takarar gwamnan Adamawa a inuwar APC, Sanata Aishatu Binani a gidanta da ke Abuja.
Bayan dakatar wasu daga cikin Kwamishinonin zabe a jihohin Najeriya, Shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa don korarsu su guda uku.
Gobara ta tashi a gidan man MRS kusa da filin jirgin Yola, yayin da wasu tankoki biyu na man fetur suka kone kurmus. Jami'an kashe gobara na kokarin kashe wutar.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ki amincewa da dokar da za ta kafa sabuwar jami'ar gwamnatin tarayya a jihar Adamawa. Ya ce akwai kura-kurai a ciki.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Umaru Fintiri ya bayyana cewa tsare-tsaren tattalin arzikin gwamnatin tarayya karkashin Tinubu, su na kuntata wa talakawan Najeriya.
Jihar Adamawa
Samu kari