Abuja
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa masu zanga-zanga su guji zuwa gidajen gyaran hali da tarbiyya domin hana kokarin ba wa masu laifi damar tserewa da daga gidan.
Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba zai iya hana zanga-zanga ba saboda shi ma ya ci moriyarta.
Gwamnatin Tarayya ta bukaci matasa da su dawo daga rakiyar zanga-zanga inda ta ce ta tanadi dukkan tsare-tsare domin kawo karshen matsalolin da ake fama da su.
Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin kirkirar sabuwar sakatariya ta matasa bayan korafin matasa a Abuja inda ya ke ganin hakan zai hana su zanga-zanga.
Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa da su bude layukan da suka rufe saboda rashin sanya lambar NIN. Ta ja kunnen kwastomomi.
Yayin da wasu 'yan kasar nan su ka fara zanga zanga a Neja da babban birnin tarayya Abuja, 'yan majalisa sun sanya ranar da za su yi taron gaggawa.
Wasu matasa sun fara gudanar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya a jihar Niger. Matasan sun yi kira ga Bola Tinubu kan dawo da tallafin man fetur.
Kungiyar yarbawa ta Afenifere ta samu baraka tsakaninta, inda aka samu bangarori biyu su na adawa da juna a kan zanga-zangar adawa da manufofin shuganan kasa,.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun kafa shingen binciken ababen hawa a titin Keffi-Abuja sa'o'i 24 gabannin fara zanga-zangar tsadar rayuwa.
Abuja
Samu kari