Jami’an Birtaniya Sun Yi Watsi da Yarima Harry a Ziyarar da Ya Kawo Zuwa Najeriya

Jami’an Birtaniya Sun Yi Watsi da Yarima Harry a Ziyarar da Ya Kawo Zuwa Najeriya

  • Jami'an gwamnatin Birtaniya sun bayyana dalilansu kan nuna halin ko in kula ga ziyarar da Yarima Harry ya kawo tarayyar Najeriya
  • Hukumomin Birtaniyan sun magantu ne bayan yawaitar cece-ku-ce kan rashin jin motsin su a zahiri ko yanar gizo kan zuwan yariman
  • Yarima Harry da matarsa dai sun zo Najeriya ne tun ranar Juma'a domin gudanar da ayyuka na musamman cikin 'yan kwanaki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Jami'an gwamnatin Birtaniya da ke Najeriya sun nuna halin ko in kula ga jikan sarauniya Elizabeth II, Prince Harry Charles, yayin ziyarar da ya kawo Najeriya.

Yarima Harry da mai dakinsa, Meghan Markle, sun iso Najeriya ne tun ranar Jumu'a domin ziyarar kwana uku.

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar jihar Niger zai aurar da marayu 100

Prince Harry
Jami'an Birtaniya sun ce Yarima Harry ba karkashin gwamnati ya zo Najeriya ba. Hoto: Extra
Asali: Facebook

Tun isowarsu birnin tarayya Abuja da yammacin Jumu'ah suka samu tarba mai kyau daga jami'an sojin Najeriya, cewar jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wuraren da Yarima Harry ya ziyarta

Yarima Harry tare da matarsa sa sun ziyarci hedikwatar tsaron Najeriya da ke Abuja wanda dama tana cikin jerin wuraren da za su ziyarta.

Daga nan sun wuce jihar Kaduna inda suka gana da gwamnan jihar, Uba Sani wanda ya ba yariman kyautar babbar riga.

Harry: Jawabin hukumomin Birtaniya

Amma a bangaren hukumomin Birtaniya da suke Najeriya kuma ba a ga wani motsi da suka yi ba domin tarbar yariman wanda hakan ya saɓa ga al'adarsu.

A lokacin da suke karin haske ga 'yan jarida, hukumomin kasar ta Birtaniya sun bayyana cewa lalle su na sane da zuwan yariman Najeriya.

Amma sai dai jami'an gwamnatin sun bada dalilin cewa zuwansa Najeriya ba shi da alaka da ayyukan gwamnatin kasar Birtaniya.

Kara karanta wannan

An kama soja boye da makamai cikin buhun shinkafa a jihar Borno

Sun kuma kara da cewa ba su da wani alhaki wajen karbarsa ko tsare-tsaren ayyukan da zai gabatar a Najeriya.

Dalilin zuwan yarima Harry Najeriya

A lokacin da yariman ya ziyarci jihar Kaduna ya bayyana cewa babban makasudin zuwansa Najeriya shine ya gana da sojojin da suka yi rauni domin karfafa musu gwiwa.

Yarima Harry ya bayyana cewa harkar wasannin Invictus da aka kirkiro domin ɗebe kewa ga sojojin da suka yi rauni hanya ce da za ta kara karfafansu.

Birtaniya za ta ba 'yan Najeriya tallafin karatu

A wani rahoton, kun ji cewa daliban Najeriya na da damar neman tallafin Euro 10,00 daga gidauniyar GREAT don yin karatun PGD a jami'o'in kasar Birtaniya a zangon karatu na 2024-25.

Wannan tallafin hadin gwiwa ne tsakanin gidauniyar GREAT Britain da kuma hukumar kasar Birtaniya, da suka shafi jami'o'in Ingila, Wales, Scotland da Ireland ta Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel