Abba Gida-gida
Sanata Barau Jibrin ya ce yanzu haka NNPP na raguwa a Kano kuma manyan 'yan Kwankwasiyya za su sauya sheka a gaba kadan. Ya fadi haka yayin karbar a'yan NNPP.
Kungiyar tsofaffin 'yan majalisar dokokin jihar Kano ta nada Sanata Barau Jibrin matsayin uban kungiya. Barau Jibrin ya ce zai cigaba da aiki domin kawo cigaba.
Jam'iyyar NNPP ta musa ikirarin da Shugaban APC, Abdullahi Ganduje na cewa Rabiu Kwankwaso zai koma APC bayan mutuwar NNPP. NNPP ta ce zancen ba gaskiya ba ne.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da rasuwar mai taimakawa Gwamna Abba Kabir Yusuf a bangaren matasa, Hon. Abdullahi Salisu Furfura a jihar Kano.
Dan daba da aka fi sani da Abba Dujal ya mika wuya ga 'yan sandan jihar Kano. Dujal ya ce ya kashe mutane a Kano da Jigawa, ya sace babura da wayoyin jama'a.
Rundunar ‘yan sanda a Edo ta ce an cafke mafarauta hudu daga Kano da makamai yayin da suka isa jihar ranar Asabar da dare a dakin hotel da ke jihar.
Gwamnatin Kano ta sauke nauyin bashin da ake bin jihar na karatun dalibai 84 da gwamnatin baya, a karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta aika kasar waje karo karatu.
Bayan dawowa daga Edo, mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tabbatar da cewa yan Arewa da ke zaune a Edo suna cikin aminci da kwanciyar hankali.
Gwamna Monday Okpebholo ya ce gwamnatinsa da ta tarayya sun kafa kwamitin bincike don gano musabbabin kisan matafiya 16 'yan Kano a Uromi, jihar Edo.
Abba Gida-gida
Samu kari