Yan ta'adda
Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan ta'adda da ake zargin na Boko Haram/ISWAP ne sun sace wani babban farfesa a jami'ar NAUB tare da wasu fasinjoji.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fito ta karya rahotannin da ke yawo masu cewa yan ta'adda sun samu mafaka a birnin tarayya Abuja. Ta ce babu kamshin gaskiya a ciki.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a yakin da suke yi da 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno. Sojojin sun hallaka babban kwamandan kungiyar.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta zuba idanu wasu tsirarun 'yan siyasa suna kokarin jefa rayuwar jama'a a masifa ba.
Dalibar Jami'ar Tarayya ta Gusau a jihar Zamfara mai suna Zarah Abubakar Shehu, mai shekaru 21 ta mutu bayan an biya fansa har N10m da wasu kayayyaki.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da wasu shugabannin APC biyar daga Kaura Namoda ta Kudu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani fitaccen ɗan bindiga a jihar Katsina, Abu Radde da yaransa sun miƙa wuya ga jami’an tsaro inda suka saki mutum goma.
‘Yan bindiga sun kashe manoma 9 a yankin Karaga, inda suka sace mutane 6 a Farin-Doki, tare da kwashe shanu. Halin tsaro a Neja na kara tabarbarewa.
Rundunar tsaron Najeriya ta kashe 'yan ta'adda 217, ta kama 574 tare da ceto mutane 320 a watan Fabrairu. 'Yan ta'adda 152 ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya.
Yan ta'adda
Samu kari