Yan ta'adda
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da halaka wani ‘Dan bindiga tare da kama wasu shida da ake zargi. Suna daga cikin yaran Bello Turji da Kachalla.
'Yan bindiga sun tare a wani dajin jihar Bauchi, inda suke sace mutane suna yin karbar kudin fansa. An kuma kama wasu da ake zargi da yin garkuwa da mutum hudu.
Wasu miyagun ‘yan bindiga sun kai farmaki kan matafiya a babbar hanyar Lokoja zuwa Obajana inda suka harbi wani fitaccen ‘dan jarida. An garzaya dasu asibiti.
Dakarun rundunar sojojin sama sun yi gagarumin nasara a kan mayakan Boko Haram inda suka kashe kwamandoji uku da mayaka 30 tare da jikkata wasu 40 a Borno.
Wani rahotan jaridar Vanguard ya hakaito abubuwan da suka faru na tashin-tashina da rashin tabbas a wannan shekarar ta 2022 ta muke daf da bankwana da ita.
Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya roki jami’an tsaro da su dage kada su har kasar nan hannun ‘yan ta’adda. Ya roki jama’a da su basu hadin kai don tsaro.
Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya dake Abuja ta kama wata kungiyar 'yan bindiga da suka addabi yankunan Abuja da Nasarawa da wasu miyagun makamai.
'Yan bindiga sun kai farmakin kwanaki uku a jere a wasu yankunan jihar Sokoto na tsawon kwanaki uku inda suka dinga halaka jama'a tare da garkuwa da sama da 50.
Dakarun ‘yan sanda a jihar Ogun sun kubutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi. Wannan mutumi ya ga ta kan sa tun da aka yi damfara, amma ya dauke kudin.
Yan ta'adda
Samu kari