Yan ta'adda
Yayin da hukumomi ke ta kokarin dakile ta'addanci a Najeriya, kungiyar ISWAP ta kammala shirye-shirye domin bude gidan rediyo ta yanar gizo domin yaɗa manufofi.
An samu asarar rayuka bayan an gwabza fada a tsakanin 'yan bindiga da 'yan banga a jihar Sokoto. Mutane da dama sun rasa rayukansu a dalilin arangamar.
A yayin da jami'ar jihar Filato ta sanar da rufe makarantar na kwanaki 10, gwamnan jihar Mutfwang ya yi Allah-wadai kan harin da aka kai jami'ar da ke Bakkos.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana dalilan da suka haddasa matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya.
Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Taoreed Lagbaja, ya ja kunnen 'yan ta'adda da sauran masu son kawo rashin zaman lafya da tada zaune tsaye a kasar nan.
'Yan bindiga masu gaba da juna sun yi mummunan artabu a jihar Zamfara Fadan ya jawo an hallaka shugabanni biyu da mayaka 12 a karamar hukumar Tsafe.
Akalla mutum 10 aka tabbatar da sun mutu sakamakon wani bam da ya tashi da motar Bas ta haya a kan titin Baga-Kokawa a ƙaramar hukumar Kokawa a Borno.
Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da kama yan daba da aka fi sani da yan shila a jihar. Mata biyu na daga cikin wadanda rundunar ta cafke
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto wata daga cikin 'yan matan Chibok da ke tsare a hannun Boko Haram. Dalibar ta shafe shekara 10 a tsare.
Yan ta'adda
Samu kari