Rundunar 'Yan Sandan Adamawa ta Kama 'Yan Shila 49

Rundunar 'Yan Sandan Adamawa ta Kama 'Yan Shila 49

  • Rundunar 'yan sandan Adamawa ta tabbatar da kama 'yan daba da aka fi sani da 'yan shila da suka addabi sassa daban-daban na jihar a wani samame da suka kai
  • Suleiman Nguroje, kakakin rundunar ne ya tabbatarwa manema labarai da kamen, inda ya ce cikin yan shilar da aka kama akwai mata biyu
  • Rundunar 'yan sandan ya nemi hadin kan al'umma ta hanyar ba su bayanan sirri na shawagin duk wasu da ba su aminta da su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Adamawa, Yola- Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da cafke ‘dan daba da aka fi sani da ‘yan shila a wurare daban-daban a babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Ana murna Dangote ya fara fitar da mai, sojoji sun tafka ta'asa a matatar, an dauki mataki

Jami’in hulda da jama’a na rundunar 'yan sanda jihar, Suleiman Yahaya Nguroje ya shaidawa manema labarai cewa jami’anta sun kama ‘yan shilan ne a wani samame da suka kai sassa daban-daban a jihar.

Yan shila49rundunar yan sandan ta kama
Cikin yan Shila da rundunar yan sandan ta kama akwai mata guda 2 Hoto: Suleiman Yahaya
Asali: Facebook

'Yan shila sun shiga hannun 'yan sanda

Daga wadanda aka kama akwai mata guda biyu da suka kware wajen takurawa al’umma, kamar yadda Leadership News ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nguroje ya bayyana cewa sun cafke ‘yan shilan da suka sha kai hare-hare sassa da dama a yankunan Geriyo Junction, Doubeli Junction da Jambutu Aso Rock.

Ana da labarin hare-haren na su a bayan kwalejin Ramat da gadar sama dake total, kamar yadda Tribune Online ta wallafa.

Rundunar 'yan sandan ta nemi taimakon al’ummar gari da bayanan sirri a duk lokacin da suka ga bata-gari na shawagi a kusa da su, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanya dokar ta baci da umarnin harbe 'yan daba a Arewacin Najeriya

'Yan Sanda sun kama bata-gari a Adamawa

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa Suleiman Nguroje ya bayyanawa manema labarai cewa wasu kasungurman masu garkuwa da mutane da suka addabi jihar sun shiga hannu.

Ya bayyana cewa bayanan sirrin da suka samu daga al'umma ne ya tallafa musu wajen kama bata-garin da suka dade suna kai hare-hare sassan jihar, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Cikin wadanda aka kama akwai Ahmed Muhammad mai shekaru 37 mazaunin karamar hukumar Song; da Muhammed Haruna mai shekaru 25 mazaunin Jambutu, karamar hukumar Yola ta Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel