Shugaban Sojojin Kasa Ya Aika da Sabon Gargadi Ga 'Yan Ta'adda

Shugaban Sojojin Kasa Ya Aika da Sabon Gargadi Ga 'Yan Ta'adda

  • Taoreed Lagbaja wanda ke shugabantar sojojin ƙasa na Najeriya, ya ja kunnen ƴan ta'adda da masu tada ƙayar baya
  • Lagbaja ya bayyana cewa dakarun sojojin ƙasar nan ba za su saurara ba har sai sun ga bayan ƴan ta'addan da sauran masu son kawo rashin zaman lafiya
  • Ya kuma buƙaci sojoji da kada nasarar da ake samu a kan tsagerun ta sanya su yi sanyi domin har yanzu akwai sauran rina a kaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya sha alwashin cewa rundunar sojojin Najeriya ba za ta saurara ba har sai ta ga bayan ƴan ta'adda.

Lagbaja ya kuma ja kunnen masu aikata laifuka da sauran masu son kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasar nan da su shiga taitayinsu ko su fuskanci hukunci.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta, sun kashe bayin Allah sama da 20 a Kaduna

Lagabaja ya gargadi 'yan ta'adda
Taoreed Lagbaja ya ja kunnen 'yan ta'adda Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Lagbaja ya yi wannan gargadin ne a wajen rufe taron hafsan sojojin ƙasar nan na shekarar 2024 a Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane gargaɗi Lagbaja ya yi wa ƴan ta'adda?

"Ina son na gargaɗi masu aikata laifuka a cikin al'ummarmu cewa rundunar sojojin Najeriya ba za ta saurara ba har sai ta sheƙe su."
"Ina kira ga ƴan Najeriya masu bin doka ds oda da su goyi bayan rundunar mu a ƙoƙarin da muke yi na samar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi."

- Taoreed Lagbaja

Lagbaja ya kuma gargaɗi dakarun sojojin da kada nasarorin da ake samu a kan ƴan ta'adda a ƙasar nan ya sanya su yi sanyi, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya yi nuni da cewa tun da har yanzu ba kammala cin nasara ba, lokacin yin murna bai yi ba.

Kara karanta wannan

Kano: Ana fargabar mutum 45 sun rasa rayukansu sakamakon barkewar sabuwar cuta

Ya kuma buƙaci dakarun sojojin da su zama masu ƙwarin gwiwa a wajen yaƙi da rashin tsaro,.inda ya yi nuni da cewa idan suka nuna tsoro ƴan ta'adda za su samu ƙarin ƙarfin gwiwar aikata laifuka.

Za a ginawa sojoji gidaje

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin ƙasar nan ta kammala shirin ginawa sojojin dake bakin daga gidaje domin su samu wurin zama bayan sun yi ritaya.

Rundunar ta kuma ƙara da ninka kuɗin inshorar sojojin a wani shirin ko-ta-kwana da take yi domin kulawa da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel