An Sheke Shugabannin 'Yan Bindiga 2 a Wani Kazamar Fada a Jihar Zamfara

An Sheke Shugabannin 'Yan Bindiga 2 a Wani Kazamar Fada a Jihar Zamfara

  • An gwaba ƙazamin faɗa a tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga uku a jihar Zamfara wanda ya jawo aka samu asarar rayuka masu yawa
  • A mummunan artabun dai an hallaka shugabannin ƴan bindiga biyu, Kachallah Gwande da Ƙachallah Madagwal tare da mayaƙa mutum 12
  • Ƴan bindiga da dama kuma sun samu munanan raunuka sakamakon gwabzawar da aka yi a ƙauyen Kaurar Zomo cikin ƙaramar hukumar Tsafe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - An hallaka wasu fitattun shugabannin ƴan bindiga guda biyu, Kachala Gwande da Kachallah Madagwal da wasu mutum 12 a jihar Zamfara.

Hakan ya biyo bayan arangamar da aka yi a tsakanin wasu ƙungiyoyin ƴan bindiga uku a ƙauyen Kaurar Zomo na gundumar Kunchin Kalgo cikin ƙaramar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da 'yan banga sun gwabza fada a Sokoto, an hallaka mutum 6

An hallaka 'yan bindiga a Zamfara
An hallaka shugabannin 'yan bindiga biyu a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Zagazola Makama, masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya bayyana hakan a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makama ya ce ƙungiyoyin da ke gaba da juna a rikicin su ne Alhaji Tsauni, Kachallah Jafaru, da kuma na Kachallah Gwande.

Yaushe aka yi faɗan?

An gwabza ƙazamin faɗan ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 3:45 na rana, wanda ya yi sanadin mutuwar ƴan bindiga 12 daga ɓangarorin uku.

Jafaru, wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya shahara a ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina, ya sauka a ƙauyen Kaurar Zomo, wanda ke matsayin tungar Tsauni, inda daga nan faɗa ya ɓarke.

Jafaru da mayaƙansa sun samu nasarar yin galaba kan Gwande da mayaƙansa inda suka hallaka su.

Faɗan ya ƙara ƙamari ne bayan labarin kashe Gwande ya yaɗu, lamarin da ya haifar da wani mummunan artabu da ƙungiyar Kachallah Madagwal, wanda shi ma aka kashe shi a yayin musayar wuta.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Kusan Mutum 50 a Garuruwa 3 a Jihar Katsina

Zagazola Makama ya ƙara da cewa ƴan bindiga da dama da suka samu munanan raunuka an kwashe su zuwa cibiyar lafiya ta Munhaye domin samun kulawar gaggawa.

An gwabza faɗa tsakanin ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa An gwabza mummunan sabon faɗa tsakanin mayaƙan ƙungiyoyin ta'addanci na ISWAP da Boko Haram.

Ƙazamin faɗan da ƴan ta'addan suka yi ya jawo an yi asarar rayukan mayaƙa masu yawa daga ƙungiyoyin biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel