Rashin Tsaro: Mazauna Kauyen Zamfara Sun Nemi Mafaka a Gidan Gwamnati

Rashin Tsaro: Mazauna Kauyen Zamfara Sun Nemi Mafaka a Gidan Gwamnati

  • Al'ummar garin Bini sun yi tururuwa zuwa gidan Gwamnatin jihar Zamfara domin neman mafaka daga harin 'yan bindiga
  • Mutanen sun ce sun bar ƙauyensu ne bayan janye sauran sojojin dake basu kariya daga ƴan bindigar a yau Lahadi
  • Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba za ta taɓa yin sulhu da ƴan bindigar da ke kai hari ba, kuma za ta tsare rayukansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Zamfara-Ɗaruruwan al'ummar ƙauyen Bini dake ƙaramar hukumar Maru a Zamfara ne su ka yi gudun hijira zuwa gidan gwamnatin jihar don neman mafaka daga ƴan bindigar da su ka hana su sakat.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Kusan Mutum 50 a Garuruwa 3 a Jihar Katsina

Mutanen, wadanda mafi yawansu mata ne da ƙananan yara sun ce dole su bar ƙauyensu biyo bayan janye dakarun sojin dake ba su kariya.

Gwamna Dauda Lawal Dare, Zamfara
Mazauna garin Bini sun gudu gidan gwamnatin Zamfara saboda fargabar harin ƴan bindiga Hoto: UGC
Asali: UGC

Wani mazaunin garin wanda ya yi hijira tare da matan ya ce ƴan bindiga sun kashe da yawa daga sojojin dake jibge a ƙauyen, inda a yau ne kuma aka janye sauran ke ba su kariya, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani Malam Umar Salisu, ya shaidawa manema labarai cewa:

"Yanzu babu jami'an tsaro a yankunan mu, shi yasa mu ka yanke shawarar tahowa gidan gwamnati da matanmu da yaranmu domin samun mafaka."

"Mun ƙi yarjejeniya da ƴan bindiga," Gwamnati

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ƴan ta'addar na ƙara matsa ƙaimi wajen kai hare-hare saboda ta ƙi yin sulhu da su.

Da ya ke ganawa da dandazon jama'ar a madadin gwamnatin Zamfara, Kwamishinan ilimin kimiyya da fasaha a jihar, Alhaji Wadatau Madawaki ya ce gwamnati ba za ta taɓa yin sulhu da ƴan bindigar ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta, sun kashe bayin Allah sama da 20 a Kaduna

A rahoton da PM News ta wallafa, ya roƙe mutanen su ci gaba da haƙuri, domin gwamnatin Dauda Lawal na ƙoƙarin shawo kan matsalar rashin tsaro.

Matasa sun yi zanga-zanga a Zamfara

Mun kawo muku yadda wasu fusatattun matasa a jihar Zamfara su ka yi zanga-zanga domin nuna baƙin cikin yadda ƴan bindiga ke ci gaba da kashe mazauna Tsafe.

Duk da dai jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga, mutanen Tsafe ma zargin ƴan sanda da ƙin yin wani kataɓus yayin da ƴan bindiga su ka yi sanadin rasuwar mutane 3.

Asali: Legit.ng

Online view pixel