Yan ta'adda
'Yan ta'addar Boko Haram sun kai mummunan hari jihar Borno sun kashe manoma 40. Boko Haram sun mamaye kauye suna harbi kan mai uwa da wabi yayin harin.
Tsagerun 'yan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a jihar Borno. 'Yan ta'addan sun hallaka mutane tare da kona gidaje masu yawa a harin da suka kai.
Gwamna Dauda Lawal ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa ransu dalilin harin sojoji inda ya yaba wa kokarin sojojin a sabon farmakin da suka kai kan 'yan bindiga.
Yayin da sojoji ke ci gaba da kai farmaki kan yan bindiga, an ce shugaban yan ta'adda, Ado Aliero ya rikice gaba daya inda yake gudu ƙauyuka daban-daban.
Rundunar sojojin Najeriya ta bai wa dakarunta da ke fafatawa a fagen fama umarnin kawar da 'yan ta'addan Lakurawa ko kuma fatattakarsu daga kasar bakiɗaya.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce jami'an sojoji sun yi nasara kan ƴan ta'adda a Operation daban-daban da suka kaddama cikin mako guda a ƙasar nan.
Rahotanni sun tabbatar an gano dan ta'adda Bello Turji da yaransa sun kwana suna dasa wasu abubuwa a kusa da duwatsun Fakai da Manawa don kare kansu daga hare-hare.
Mayakan Boko Haram sun kai hari a ofishin 'yan sanda na Borno inda suka kashe jami'ai biyu. An ce wasu gurnetin hannu biyu da mayakan suka jefa ya yi kashe jami'an.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da kai hari wasu kauyukan jihar Imo inda aka yanka mutane 18 a karamar hukumar Orsu. An kashe mutanen an barsu cikin jini.
Yan ta'adda
Samu kari