'Ku Sake Zaɓen Tinubu': APC Ta Faɗi Ɓangarori 4 da Zai ba Muhimmanci

'Ku Sake Zaɓen Tinubu': APC Ta Faɗi Ɓangarori 4 da Zai ba Muhimmanci

  • APC ta ce tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya zai kasance babban abin da Tinubu zai mayar da hankali a kai idan ya sake lashe zaɓen 2027
  • Jam’iyyar ta yi alƙawarin ɗaukar ƙarin sojoji 28,000 da ’yan sanda 50,000 domin ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane
  • APC ta kuma bayyana manufofinta guda huɗu na 2027, ciki har da samar da wutar lantarki, inganta tattalin arziki da rage talauci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Jam’iyyar APC ta bayyana cewa tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya zai kasance babban abin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ba fifiko idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairun 2027.

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta ɗauki ƙarin jami’an tsaro 78,000, waɗanda suka haɗa da sojoji 28,000 da ’yan sanda 50,000, domin ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

An nada alkalai 375 domin sauraron kara bayan zaben 2027

APC ta yi alkawari sauya Najeriya bayan zaɓen Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin zaman majalisar zartarwa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Mataimakiyar daraktar kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC mai kula da tsara manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar, kuma Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, ce ta bayyana hakan a Abuja, cewar Vanguard.

Ta yi jawabi ne yayin gabatar da manufofin jam’iyyar na zaɓen 2027, ƙarƙashin taken sauya sheƙa daga gyare-gyaren tattalin arziki zuwa wadata da kowa zai amfana da ita.

APC ta yi alƙawarin yaƙi da ’yan bindiga

Baya ga ɗaukar ƙarin jami’an tsaro, APC ta ce za ta kammala gina sansanonin rundunonin sojoji huɗu da aka ƙaddamar a Makurɗi, Ilorin, Jalingo da Benin City tare da samar musu da kayan aiki.

Jam’iyyar ta kuma yi alƙawarin ci gaba da kai hare-hare bisa sahihan bayanan sirri kan ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane domin rusa sansanoninsu.

Haka kuma, APC ta ce za ta tura jami’an tsaron da aka horas musamman domin kula da dazuzzuka, da suka haɗa da Forest Guards, Agro-Rangers da Mining Marshals.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta ragargaji APC kan hukuncin rusa takarar Atiku a kotu

Jami’an za su mayar da hankali wajen kare gonaki, al’ummomin manoma, hanyoyin kiwo, dazuzzukan gwamnati da wuraren da ake haƙar ma'adanai.

A cewar Oduwole, burin gwamnatin APC shi ne mayar da Najeriya ƙasa mai cikakken tsaro, inda kowa zai samu damar gudanar da rayuwarsa da cimma burinsa ba tare da fargaba ba.

Gbajabiamila ya shawarci yan Najeriya kan APC

A nasa jawabin, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya buƙaci ’yan Najeriya su karanta manufofin APC na baya da na yanzu, sannan su yi wa jam’iyyar hukunci bisa abubuwan da ta aiwatar tun bayan karɓar mulki a 2023.

Gbajabiamila ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun jefa iyalai cikin matsin rayuwa, yana mai cewa ya kamata a saurari koke-kokensu.

Ya ce bambancin ɗan siyasa da shugaba shi ne yadda ɗan siyasa ke tunanin zaɓe na gaba, yayin da shugaba ke la'akari da makomar al'ummar da yake jagoranta.

Ya ce wannan shi ne abin da Tinubu ya nuna ta hanyar ɗaukar matakan gyara tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya yi wa yankin Tinubu gori kan kuri'u, ya bugi kirki kan Arewa

Manufofin APC guda huɗu na zaɓen 2027

Gbajabiamila ya bayyana cewa manufofin APC na zaɓen 2027 sun ta'allaka ne kan manyan ginshiƙai guda huɗu.

Ginshiƙan sun haɗa da:

1. Samar da ƙasa mai cikakken tsaro da juriya wajen fuskantar matsaloli.

2. Inganta rayuwar ’yan Najeriya da rage tsadar abubuwan buƙata.

3. Samar da makamashi, inganta ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.

4. Samar da gwamnati mai inganci da riƙon amana.

Ya ce waɗannan manufofi za su taimaka wajen aiwatar da manyan muradun Renewed Hope Agenda na gwamnatin Tinubu.

APC ta magantu kan kuri'un Kiristoci

An ji cewa Nentawe Yilwatda ya ce Kiristoci da dama sun amince da tikitin APC na Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima.

Ya ce babu Kiristan da aka tauye wa haƙƙinsa ko aka muzanta saboda addininsa a cikin shekaru uku na gwamnatin Tinubu.

Yilwatda ya ambaci kansa, George Akume da Christopher Musa a matsayin Kiristocin Arewa da ke riƙe da manyan muƙamai a gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.